Hukumar yan sandan NAjeriya
Yan sanda a jihar Ribas sun kama sojoji da jami'an NSCDC da fashi da makami da sace babbar mota dauke da kayan abinci. Rundunar soji ta kori jami'anta da aka kama.
Jama'a sun shiga ɗimuwa bayan jin karar harbe-harbe masu tayar da hankali daga fadar Nasarawa inda Sarkin na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune a jihar Kano.
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya faɗawa shugabannin tsaro cewa a soshiyal midiya kaɗai ake yaɗa umarnin kotun da ta ce kar a naɗa shi sarki.
Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cewa an samu rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar. Mutum biyar sun raunata.
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta musanta labarin cewa 'yan ta'addan da suka kai hari jihar sun kashe mutane 40 kamar yadda aka yayatawa a wasu wuraren.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta gano shirin tayar da tarzoma a jihar da wasu bata gari ke yi. Ta yi gargadin cewa za ta cafke duk masu hannuna shirin.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya ta sanar da cewa ƴan bindiga sun yi ajalin daliban Jami'ar jihar da suka sace a farkon wannan wata.
An shiga jimami bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde wanda ya rasu a kasar Masar yayin da yake jinya yana da shekaru 61.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kaduna sun samu nasarar cafke wani kasurgumin dan bindiga a jihar. Jami'an tsaron sun kuma ceto mutum uku da aka sace.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari