Hukumar Kwastam na Najeriya
Jami'an hukumar hana fasakwauri ta bayyana dakile yunkurin shigo da buhunhunan shinkafa 'yar waje akalla 6,467 ta iyakar Seme wanda ya kai tirela 10.
Hukumar kwastam ta fitar da abubuwan da ta kama daga watan Janairu zuwa Afrilu. Ta sanar da kama na'urorin kirifto, kudaden bogi da makamai masu yawa.
Hukumar NDLEA ta yi nasarar kamawa da lalata miyagun kwayoyi a jihohin Legas da Ogun. Shugaban hukumar ne Buba Marwa ya bada sanarwar ranar Talata
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar hana fasa kwauri ta kasa watau Kwastam, da ta mayar da kayan abincin da ta kwace ga mutanen da ke da su.
Shugaban hukumar kwastam ta ƙasa, Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa tuni suka fara siyar da kayan abinci ga masu ƙaramin karfi domin fatattakar yunwa.
Kwastam ta ce kusan N200m ake samu a kowace sa'a watau kusan N5bn kenan a wata daga tashar Apapa. Duk ranar Allah sai jami’an sun tatsi Naira Biliyan 4 a tashar.
Hukumar kwastam ta Najeriya (NSC) ta dakatar da siyar da kayayyakin abincin da ta ƙwace a farashi kai rahusa saboda abinda ya faru a jihar Legas makon jiya.
An samu turmutsitsi a wajen siyan kayan abinci da hukumar kwastam ke siyarwa talakawan Najeriya don rage radadi. Mutum bakwai sun rasa ransu a jihar Legas.
Hukumar kwastam ta ayyana cewa daga ranar 23 ga watan Fabrairu,m za a fara siyar da shinkafa da sauran kayan abinci ga talakawa a Legas da sauran sassa na kasar.
Hukumar Kwastam na Najeriya
Samu kari