Musulmai
Babban limamin Agaie, Sheikh Muhammadu Kudu ya rasu. Gwamna Umaru Bago ya ce mutuwar ra girgiza al'ummar jihar Neja baki daya. An masa addu'o'in samun aljanna.
Majalisar koli ta addinin Musulunci, NSCIA ta bayyana goyon bayanta ga shirin 'Qur'anic festivcal' da wasu daga cikin Musulmi ke ganin ya saba da koyarwa addini.
Idan yanayi ya canja ana samun canji a lokutan salla a Najeriya, Simwal Auwal Jibril ya bayyana hanyoyin da za a bi wajen bin sallar La'asar da Magriba kan lokaci.
Malamin a jami'ar Legas, Farfesa Tajudeen Yusuf ya haddace Kur'ani yana shekaru 59 a duniya. Ya yi kira ga al'ummar Musulmi su rungumi karatun Kur'ani.
Sheikh Sharif Saleh ya buƙaci kafafen watsa labarai su maida hankali kan muradan ƙasa da shugabanci na gari domin su ne idanu da kunnuwan al'umma.
Wata kotu a ƙasar Iran ta yanke wa mawakin nan, Amir Hossein Maghsoudloo hukuncin kisa bayan kama shi da laifin taɓa mutuncin Annabi Muhammad SAW.
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ba za ta lamunci rashin tarbiyya da take dokokin addinin Musulunci da wasu 'yan Kannywood ke yi da sunan sana'a ba.
NAHCON ta amince da Naira miliyan 8.7 a matsayin kudin aikin Hajjin 2025 ga maniyyatan Kudu, sai Naira miliyan 8.3 ga 'yan Arewa maso Gabas. Ta yi karin bayani.
Mazauna Gangare sun sake dawowa garuruwansu bayan shekaru 20 da rikicin Jos, suna fatan dawo da zaman lafiya. Fasto da Limamai sun yi kira ga haɗin kai da juna.
Musulmai
Samu kari