Masu Garkuwa Da Mutane
Yan bindiga sun kai sabon farmaki gundumar Kawu da ke karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da mutane 23.
Wasu 'yan bindiga biyu a jihar Taraba da suka shahara wajen garkuwa da mutane don kudin fansa sun saduda tare da mika wuya ga 'yan doka. Suna son zama 'yan banga.
Ganin yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta'azzara, Sheikh Aminu Daurawa ya ba gwamnatin Shugaba Tinubu satar amsa, kan hanyar kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
Jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun cafke mai garkuwa da mutane Samaila Wakili Fafa wanda aka fi sani da Abu Ibrahim a dajin Sardauna.
Yan sanda tare da haɗin guiwar mafarauta sun shiga har cikin daji, sun sheke yan bindiga masu ɗumbin yawa tare da kwato mutane 40 da aka sace a Taraba.
Wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne dauke da makamai sun yi awon gaba da mutane biyar da aka shirya za su ba da shaida a kan zaben gwamnan Kogi.
A wani kazamin rikici da ya barke a Zamfara, kungiyar Ado Allero ta kashe akalla manyan ‘yan bindiga biyar da mayakan su 48. Yan bindiga na neman Allero ruwa a jallo
Mummunan harin sojoji ya ga bayan wasu shugabannin ‘yan bindiga. Sojoji sun cigaba da murkushe ‘yan bindiga, an hallaka jiga-jigan miyagu 30 a tashi daya.
An ruwaito yadda 'yan ta'adda suka kai sabon hari a Kaduna bayan da aka kashe shugabansu a wani yankin jihar. An jima ana samun hare-hare a jihar Kaduna.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari