Masu Garkuwa Da Mutane
Akalla 'yan bindiga bakwai ne suka ajiye makaman su tare da mika wuya ga gwamnatin jihar Filato bayan zaman sulhu. An ruwaito su ne ke addabar garuruwan Wase.
Babban fasto na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da aka sace a jihar Oyo ya kubuta daga hannun 'yan bindiga bayan jami'an tsaro sun ceto shi.
An kama wata mata mai shekara 40 da take ‘satar’ kanana yara. NAPTIP ta sashen Benin, ta ce sunan matar da aka kama Ikejimba Maryvianney kuma tana karyar Fasto ce.
Miyagun ƴan bindiga sun kai sababbin hare-hare a kauyukan Batsari da Malumfashi a ranaku daban-daban a makon nan, sun sace mutane da dama a jihar Katsina.
Rahoton da muke samu daga jihar Kaduna ya nuna cewa ƴan bindigan jeji sun farmaki wani kauye a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, sun sace gomman mutane.
Taron dai na da nufin bunkasa karfin gwamnoni wajen yaki da tashe-tashen hankula da samar da zaman lafiya a fadin Najeriya ta hanyar tattaunawa da kuma hadin gwiwa.
Mutane uku a kihar Edo sun yi karyar an yi garkuwa da su ne da kuma bukatar kudin fansa. 'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin da nasarar cafke su
Wasu tsagerun ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 16 a kan titin Abuja zuwa Lokoja, sun kuma kashe direba amma an ce 6 daga ciki sun shaki iskar ƴanci.
Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana an sace yara sama da 1680 tin bayan satar 'yan makaranta na farko da aka fara a Chibok
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari