Masu Garkuwa Da Mutane
Rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom ta tabbatar da sace basarake, Ogwong A Abang a jihar a daren jiya Asabar 18 ga watan Mayu bayan sun kutsa kai cikin fadarsa.
Wata kungiya a jihar Neja ta bayyana halin da matan da yan bindiga suka kashe mazajensu suka shiga a kauyuka sama da 80 a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Yan sandar Najeriya sun kama gungun masu garkuwa da mutane a jihar Delta. Cikin mutane ukun da aka kama daya ya ce ya zo Najeriya ne daga kasar waje.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta ce ta kaddamar da farautar wadanda suka yi garkuwa da Basil Chukwuemeka, wani babban limamin cocin Katolika a jihar.
A yayin da matsalar tsaro ke kara ci wa gwamnati tuwo a kwarya, Ministan tsaro, Mohammed Badaru ya yi kira ga kungiyar tarayyar Turai da ta tallafawa Nigeria.
Tsagerun ƴan bindiga sake kai hari kauyen Yar Malamai jim kaɗan bayan jami'an tsaro sun tashi, sun sace mutane da yawa tare da tafka ɓarna ranar Litinin.
Rundunar haɗin guiwa da ta kunshi sojoji, ƴan snada, dakarun ƴan sa'kai na Radda da mafarauta sun yi nasarar ceto fasinjoji 17 daga ƴan bindiga a jihar Katsina.
Dan majalisar Zurmi da Shinkafa ya bayyana cewa al'ummar kauyuka 50 a yankin Zurmi sun gudu sun bar gidajensu saboda yawan hare-haren ƴan bindiga a kwanan nan.
'Yan bindigar sun kai hari kauyen Benue inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, tare da kashe mutane 11 ciki har da wata mata mai dauke da juna biyu.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari