Manyan Labarai A Yau
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan ya baro birnin Paris ya dawo gida Najeriya.
Sanata Ali Ndume ya fito ya sake caccakar batun mayar da hukumar FAAN da wasu ofisoshi na CBN zuwa Legas. Sanatan ya ce hakan akwai illa a siyasance.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya fito ya yi magana kan batun neman shugabancin jam'iyyar APC na kasa da aka yada cewa yana da muradi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani ma’aikacin banki, Olumide Openaike wanda ya yi karyar masu garkuwa da mutane sun sace shi saboda bashin N1.7m.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhihinsa kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya a Ekiti, ya kuma umarci ceto daliban da aka sace a jihar.
Wani dan majalisar wakilai ya kasa danne zuciyarsa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar Ekiti. Dan majalisar ya fashe da kuka yayin da ya nemi a kai dauki.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Tinubu ya yi murabus kan matsalar rashin tsaro.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai sabon farmaki a jihar Kaduna inda suka tafka sabuwar ta'asa. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da wata matar aure da 'ya'yanta uku.
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirika (CAF) ta zabi dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, domin yi masa gwajin kwaya bayan wasan Najeriya da Kamaru.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari