Manyan Labarai A Yau
Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi martani kan ficewar kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar daga kungiyar ECOWAS.
A ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, Kotun Koli ta tanadi hukunci a ‘karar da Aisha Binani ta daukaka na neman a tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.
Kungiyar lauyoyin Najeriya ta shigar da sabuwar kara a gaban kotu kan yi wa kasa hidima da Hannatu Musa Musawa, Kenny Ogungbe suka yi, wanda ta ce ya saba doka.
Dakarun sojoji da ke aikin kakkabe yan bindiga a jihar Katsina sun samu nasarar ceto mutanen da yan ta'addan suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Batsari.
Bernand Arnault ya zarce Elon Musk ya zama sabon wanda ya fi kowa kudi. A goman farko Forbes tace akwai Bill Gates, Mark Zuckerberg da Warren Buffet.
Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno wani dan Najeriya yana kuka da hawaye yayin da yake bada labarin halin da ya shiga sakamakon karayar arziki.
Majiyoyi sun lissafo dalilai uku da ake zargin sune suka sa dattawan arewa yakar gwamnatin Tinubu kan dauke manyan ofisoshin CBN da FAAN daga Abuja zuwa Legas.
Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke wani kasurgumin dan ta'adda wanda ake zargi da hannunsa a kisan da aka yi wa Nabeeha.
Wani babban jigo a jam'iyyar PDP, Richard Idowu, ya rasa ransa bayan an bindige shi har lahira a jihar Osun. Gwamna Adeleke ya umarci a gudanar da bincike.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari