Manyan Labarai A Yau
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun ziyarci al'ummar jihar Filato da hare-haren 'yan bindiga ya ritsa domin jajanta masu. Sun bayar da gudunmawar naira miliyan 100.
Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja ya sanar da aniyar gwamnatinsa na samar da sabbin jami'o'i 10 mallakin gwamnatin jihar daga yanzu zuwa 2027.
'Yan bindigar da suka yi awon gaba da daliban makaranta a jihar Ekiti sun rage kudin fansarsu zuwa naira miliyan 15.Sun yi barazanar kashe su idan ba a biya ba.
Mazauna wasu garuruwan da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna sun tsere daga gidajensu saboda fargabar harin miyagun ‘yan bindiga da suka shigo yankin.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi rashin matar mahaifinsa wacce ta rasu tana da shekara 69 a duniya. Ta rasu ne bayan ta yi jinya.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar tsaro wacce za ta yi fito na fito da ƴan bindigan da suka daɗe suna addabar jihar.
Miyagun 'yan bindigan da suka sace wasu mutum bakwai a babban birnin tarayya Abuja, sun fadi makudan kudaden fansan da za a ba su kafin su sako mutanen.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun sake kai harin ta'addanci a birnin tarayya Abuja, 'yan bindigan a yayin harin sun yi awon gaba wani babban darakta.
Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta samu nasarar yin caraf da wata mata wacce ta yi yunƙurin sayar da ƴaƴanta kan N1.8m. Ta ce dole ce ta sanya ta yin hakan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari