Manyan Labarai A Yau
Ana saura kwana daya a gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar APC kan zaben gwamnan jihar Edo, Ize-Iyamu, ya fadi dalilansa na jangewa daga takara.
Hisbah ta kama Ramlat wacce ta yi bidiyon da ta tallata kanta take cewa duk namijin da zai aure ta sai ya auro mata macen da za su dinga lalata da ita.
Wasu miyagun 'yan ta'adda dauke da bindigogi sun kai sabon farmaki a jihar Zamfara inda suka halaka mutum bakwai tare da yin garkuwa da wasu mutum 20.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi martani kan sabon mukamin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu a nahiyar Afirika.
Jami’an ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun kai samame a sansanonin masu garkuwa da mutane biyu inda suka cafke wani mutum mai suna Sa’idu Abdulkadir.
An kori jami’an rundunar ‘yan sanda uku da ke aiki da hedkwatar Zone 16 a Yenagoa, jihar Bayelsa saboda rashin da’a da aikata cin hanci da rashawa.
Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta caccaki masu sukar gwamnatin Shugaba Tinubu kan halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwar da ake ciki a Najeriya.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya umurci a gudanar da azumin kwana daya a jihar don samun saukin tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kantin Sahad da aka rufe na daya daga cikin kantuna mafi saukin kaya a babban birnin Abuja.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari