Manyan Labarai A Yau
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya kai ziyara sakatariyar jam'iyyar SDP, yayin da ake ci gaba da jita-jitar zai fice daga APC.
Sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana kan zargin daukar nauyin ta'addanci da ake yi wa Malam Tukur Mamu.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bukavi al'ummar jihar da su dage wajen yin addu'o'i ga jami'an tsaro domin kawo karshen 'yan bindiga.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da babbar murya ga 'yan majalisu da su bari ministocinsa su yi aikinsu, ta hanyar daina takura musu da yawan kira.
Wani magidanci a jihar Gombe, ya bayyana yadda yake kwashe dogon lokaci domin zuwa karbo abincin sadaka wanda zai ciyar da iyalansa idan an sha ruwa.
Dakarun sojoji sun samu nasarar sheke 'yan ta'adda mutum biyu tare da ceto mutum hudu da suka yi garkuwa da su a jihohin, Filato, Zamfara da Imo.
Kamfanin Dangote da wasu daga cikin manyan kamfanoni a Najeriya sun yi asara mai girma a shekarar 2023. Jimillar asarar da suka yi ta kai ta N1.7tr.
Jami'ar gwamnatin tarayya da ke Oye-Ekiti (FUOYE), ta koka kan yadda yajin aikin ƙungiyoyin SSANU/NASU ya jawo silar rasuwar wani dalibi a makarantar.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana sunayen mutum 15 wadanda ke daukar nauyin ta'addanci a kasar nan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari