Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya soke bikin da ya saba gudanarwa domin zagayowar ranar haihuwarsa, saboda halin da kasar nan ta samu kanta a ciki a yanzu.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana hakikanin adadin yawan daƙiban da aka sace. Gwamnan ya ce adadin dalibai 137 da aka ceto shi ne na gaskiya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi maraba da ceto daliban da aka sace a jihar Kaduna da jami'an tsaro suka yi. An ceto daliban ne bayan sun yi kwanaki a tsare.
Hedikwatar tsaro ta kasa ta fitar da bayanai kan daliban da aka ceto daga hannun 'yan bindiga a jihar Kaduna. An dai ceto daliban ne a jihar Zamfara.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kaddamar da rabon tallafin shinkafa a jihar Kano. Za a bada tallafin ne a gaba daya jihohin Najeriya.
An samu labarin rasuwar Oloro na masauratar Oro, da ke karamar hukumar Ifedoƙun a jihar Kwara. Oba AbdulRafiu Olaniyi Ajiboye ya rasu yana da shekara 70 a duniya.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da hotunan jami'an 'yan da aka kashe a wani harin kwanton bauna da aka musu a cikin dajin Ohoro da ke jihar Delta.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai sabon hari a jihar Katsina. Miyagun sun hallaka babban dan siyasa a harin da suka kai cikin watan azumi.
Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta yi wa shugaban jam'iyyar APC na kasa martani kan kalamansa na cewa jihar Anambra za ta koma hannun APC.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari