Ana Cikin Tsadar Rayuwa Gwamna Ya Ware N43bn Domin Sabon Gida da Wasu Ayyuka

Ana Cikin Tsadar Rayuwa Gwamna Ya Ware N43bn Domin Sabon Gida da Wasu Ayyuka

  • Gwamnan jihar Gombe ya gaji da zama a gidan ƙashin kansa inda ya ware kuɗi domin gina katafaren gidan gwamna na zamani
  • A yayin taron majalisar zartaswar jihar, an amince a kashe N43bn domin gina gidan da harabar babbar kotun jihar da ta majalisar dokoki
  • Majalisar ta kuma amince a kashe N10bn domin gudanar da ayyukan gina tituna a ƙananan hukumomi huɗu na jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Gombe - Majalisar zartaswar jihar Gombe a ranar Talata ta amince da kashe N43.130bn domin gina sabon gidan gwamna na zamani.

A cikin kuɗin za kuma a gina harabar babbar kotun jihar da ta majalisar dokoki, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya tura sunan ɗan Kwankwaso da mutum 3 Majalisa domin tantancewa

Gwamnan Gombe zai gina gidan N14bn
Gwamna Inuwa zai gina sabon gidan gwamna kan N14bn a Gombe Hoto: @GovernorInuwa
Asali: Twitter

An yanke wannan shawarar ne a yayin taron majalisar karo na 37 da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a shekarar 2003 lokacin da tsohon Gwamna Abubakar Habu Hashidu ya bar gidan bayan ya sha kaye, duk gwamnonin jihar da suka biyo baya, ba su zauna a gidan gwamnan da ke gidan gwamnati ba, duk da gyare-gyaren da aka yi a gidan.

A halin yanzu dai Gwamna Inuwa Yahaya yana zaune a gidansa na ƙashin kansa da ke sabuwar GRA.

Yadda za a kashe kuɗaɗen

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron, kwamishinan yaɗa labarai, Mijinyawa Ardo Tilde, ya ce majalisar ta amince da N43.130bn domin gudanar da ayyukan, rahoton jaridar Gazettengr ya tabbatar.

Da yake ƙarin haske kan ayyukan, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri, Dakta Usman Maijama’a Kallamu, ya ce za a gina katafaren ginin babbar kotun kan kuɗi N14bn.

Kara karanta wannan

Gumi ya taka rawa wurin kubutar da dalibai 137 a Kaduna? Uba Sani ya fayyace gaskiya

Za kuma a kashe N14.23bn domin gina harabar majalisar dokokin jih ar yayin da aka ware N14.9bn domin gina gidan gwamnan na zamani.

Ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da kuɗi N10bn domin gina tituna a ƙananan hukumomi huɗu na jihar, da gina gidajen jami'an hukumar GOSTEC.

Gwamna Inuwa ya bada kyauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ba ɗaliba Hajara Ibrahim Dan'azumi da kyautar kudi.

Gwamna ya ba ɗalibar kyautar kuɗi har naira miliyan biyar saboda ƙoƙarinta a gasar musabaƙa ta duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel