Labarin Sojojin Najeriya
Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji a Buni Yadi, jihar Yobe, inda suka kashe sojoji hudu, suka lalata makamai, motocin yaki da bindigogin rundunar.
An samu asarar rayuka bayan mafarauta sun gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kuma yi barna bayan sun kai wani hari a cikin kauye.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasara kan 'yan bindiga a jihar Taraba. Sojojin sun hallaka dan bindiga daya tare da kwato bindiga.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yarda da kalubalen rashin tsaron da ake fama da shi a kasar nan. Ya ce dole sai an kawo karshen matsalar rashin tsaro.
'Yan ta'addan ISWAP sun kai farmaki a wani sansanin sojoji da ke jihar Yobe. 'Ƴan ta'addan sun hallaka sojojo tare da lalata kayayyakinsu masu yawa a harin.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ba za ta saduda, ta sunkuyawa masu yunkurin tayar da hankali ba, ya ce gwamnatinsa na inganta walwar sojoji.
Kasar Birtaniya ta yi magana kan tsohon sojanta da aka kama da Bindigogi a Najeriya. An kama mutumin da bindigogi kirar AK47 fiye da 50 a jihar Delta.
Gwamnatin Borno ta ce tsananin zafin rana ne ya haddasa tashin gobara a dakin ajiye makamai na barikin sojojin Giwa, ba wai hari ba ne aka kawo daga waje.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa an samu tashin gobara a barikin sojoji da ke Giwa saboda tsananin zafi. Lamarin ya jawo tashin boma bomai a barikin.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari