Labarin Sojojin Najeriya
Rundunar sojin kasan Najeriya ta ce ta samu nasarar fatattakar wasu 'yan bindiga daga dajin karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, ta kwato makamai da babura.
Naira biliyan 33 al'ummar Tudun Biri su ke nema daga aljihun gwamnati a matsayin diyyar rayuka saboda ana tsakiyar taron maulidi sojoji sun harbawa jama'a bam.
Sojoji sun kai hare-hare akalla takwas kan fararen hula a Najeriya a cikin shekaru shida, inda abin ya fi shafar Arewacin kasar kawai. Mutane da dama sun mutu.
Wasu miyagun yan bindiga sun yi wa ayarin wasu motoci kwanton bauna a jihar Rivers. A yayin harin yan bindigan sun halaka sojoji hudu da direbobi biyu.
Gwamnatin tarayya ta neman likitoci da daliban kiwon lafiya da su shiga aikin soja don bunkasa lafiyar jami'an sojin kasar. Tinubu na shirin gina kwaleji.
Karamin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle, ya yaba wa dakarun sojoji bayan sun yi ajalin yan bindiga a kusa da Tungar Mangwaro cikin jihar Neja.
Shugaba Bola Tinubu ya ja kunnen dakarun soji da su gujewa kai hare-hare kan fararen hula, inda ya sha alwashin yin bincike kan harin Kaduna don hukunta masu laifin.
Kungiyar IMN ta ‘yan shi’a ta ce dole a tursasa gwamnatin tarayya ta gudanar da binciken musamman a kan abin da ya faru a Tudun Biri da aka kashe jama’a.
Za a ji labari ‘Yan Majalisar Arewa za su bada gudumuwar N350m a sakamakon harin sojoji a Tudun Biri. Shugaban majalisa da ‘yan majalisar Kaduna sun bada N45m.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari