Kasar Saudiya
Labarai sun zo cewa an jefo bam, an kashe mutane a lokacin sahur a Gaza. sojojin Israila sun bude wuta inda suka hallaka mutanen Gaza da ke zaune a wani gida.
An sanar da ganin watan Ramadana a kasar Saudiyya, al'ummar Musulmi za su fara Azumi a kasashen duniya daban-daban. An sanar da hakan ne a yau Lahadi.
Ana ci gaba da duban watan Azumi a Najeriya, yayin da a kasar Saudiyya tuni aka sanar da an ga watan mai alfarma, za a fara azumi a ranar Litinin din nan.
Azumin Ramadan na farawa daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, kuma yana ɗaukar daga sa'o'i 12 zuwa 17, ya danganta da inda mutum ya ke rayuwa a duniya.
Fadar shugaban kasa ta fito ta yi magana kan rahotannin da ke yawo dangane da batun cire takunkumin hana 'yan Najeriya biza da kasar UAE ta yi a baya.
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa, a matsayin jagora kuma Amirul Hajj na aikin Hajjin 2024.
Hukumar kwallon kafa ta kasar Saudiyya ta dakatar da dan wasan kungiyar Al Nassr, Cristiano Ronaldo kan nuna rashin da'a yayin wasa a karshn mako.
Gwamna Muhammad Yahaya na jihar Gombe ya nuna farin cikinsa da nasarar matashiya Hajara Ibrahim daga jihar a gasar musabaka ta duniya da aka yi a Jordan.
Ma'aikatar kasashen waje a Najeriya ta yi martani yayin da ake ta yada jita-jitar cewa Qatar ta ki amincewa da ganawa da Tinubu, kan wani taro ta musamman.
Kasar Saudiya
Samu kari