Jihar Kano
Guda daga cikin jiga-jigan jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa jama’a ba su fahimci bayanin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kan takara da Obi ba.
Gwamnatin Kano ta mika sakon jaje ga yan kasuwar Kantin Kwari da wuta ta komawa kayan da ake zaton sun kai na biliyoyin Naira, tare da daukar alkawarin taimakawa.
Dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya ce 'yan jam’iyyar NNPP a jihar Kano suna sauya sheka zuwa APC saboda gwamnatin Abba Yusuf ta gaza ta kowane fanni.
A wannan rahoton, za ku ji yadda gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sake samun lambar girmamawa kan muhimmin aikin da ya ke gudanarwa a bangaren ilimi.
Mai martaba sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi takaicin iftila'in gobara da ya afkawa wasu shaguna a Kantin Kwari da ke jihar tare da lakume dukiyoyi.
An samu tashin gobara a babbar kasuwar Kantin Kwari da ke jihar Kano a daren ranar Asabar. Gobarar wacce ta tashi, ta lakume shaguna masu yawa a kasuwar.
Akwai manyan ‘yan siyasar Kano da ke goyon bayan Bola Ahmed Tinubu yayin da hankali ya karkata kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ke tafe nan da watanni 28.
Nuhu Ribadu ya kara tada wutar rikicin sarautar Kano da ake ta yi. Amma an ji yaron Muhammadu Sanusi II ya tanka Ribadu bayan kiran Aminu da Sarkin Kano.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya ce nan ba da daɗewa ba za a nemi jar hula a kan Kanawa a rasa saboda duk sun bar Kwankwasiyya.
Jihar Kano
Samu kari