
Jihar Kano







Majalisar malaman jihar Kano ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakan da suka dace kan matsalar rikicin Kano ba tare da jawo matsala ba.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan dawo da shi sarautar Kano. Sarkin ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai tsoma baki ba.

Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara a bangaren harkokin tsaro, Nuhu Rubadu ya karyata cewa yana da hannu game da dawo da Aminu Ado Bayero jihar Kano.

Yayin da ake zargin tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya koma gida da daddare, Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinan ƴan sanda ya kama shi nan take.

Tsohon kwamishina a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Mu’azu Magaji ya bayyana cewa ana ta shirye-shiryen raka sarki Aminu Ado Bayero fadarsa dake kofar kudu.

Rahotannin da. ke fitowa sun nuna cewa yanzu haka jami'an tsaro sun mamaye wurare masu muhimmanci a gidan gwamnatin jihar Kano, ba su hana shige da fice ba.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya isa fadarsa da ke birnin inda ya ke maraba da dandazon Kanawa da suka zo fadar domin tarbarsa duk da halin da ake ciki yanzu.

Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa yanzu haka daraktan DSS da wasu manyan shugabannin hukumomin tsaro a Kani sun koma cikin fadar da Sanusi yake.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Muhammed Usaini Gumel ya bayyana cewa har yanzu suna bin umarnin kotu da ta hana gwamnatin Kano nada sabon sarki.
Jihar Kano
Samu kari