Babban kotun tarayya
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar zai rahoton alkalin ɗa ya yi koƙarin hana naɗin Sarki Muhammadu Sanusi II gaban kungiyar gwamnoni NGF.
Wata kotu a jihar Ekiti ta bada umurnin rataye wasu masu kwacen waya su biyu. An kama mutane dauke da makamai da wayoyi da kudi da suka sace a wajen wasu mutane.
Kotun sauraran kararrakin zaben jihar Imo ta tabbatar da nasarar Gwamna Hope Uzodinma na jami'yyar APC a matsayin zaɓabben gwamnan jihar a yau Juma'a.
Shari’ar da gwamnatin Najeriya ke yi da jami’in Binance, Tigran Gambaryan, a kotun tarayya da ke Abuja, taa dauki wani salo bayan Gambaryan ya yanke jiki ya fadi.
Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai shari’a Liman ta bayar da umurnin hana gwamnatin jihar Kano mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.
Rundunar yan sandan jihar Legas ta sanar da kama wani mutum mai suna Charles Chukkwudi mai karyar aikin dan sanda da kuma aikin kotu. An gurfanar da shi a kotu.
Tsohon darakta janar na kungiyar gwamnonin jihohin APC na PGF, Salihu Lukman ya yi barazanar maka jam’iyyar APC gaban kotu bisa karya kundin tsarin jam’iyyar.
Babbar kotun jihar Oyo ta yi hukunci a karar dalibai mata na makarantar International School ta jami'ar Ibadan suka shigar kan 'yancin sanya hijabi.
Mahaifi ya kai dansa kara kotu a Kano saboda matsalar sata da shaye-shaye, ya bukaci alkalin kotun ya masa daurin rai da rai. Kotun ta daga shari'ar zuwa watan Yuni.
Babban kotun tarayya
Samu kari