Nade-naden gwamnati
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya nada Sani Ahmadu Ribadu, wanda ya kasance kani ne ga Malam Nuhu Ribadu, matsayin sabon Sarkin Fufore.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya amince da naɗin sababbin manyan sakatarori dindindin 45 a bangarori daban-daban na gwamnatinsa, ya kafa tarihi.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa an samu matsala tsakanin Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo, da Wazirinsa, Muhammadu Badamasi a fada.
A wannan rahoto da muka tattaro, za a ji bankin CBN ya fadi dalilin ma’aikata 1000 na ajiye aiki a Najeriya watanni bayan an maida wasu ofisoshi zuwa Legas.
A wani lamari na bazata, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sallami Sakataren Gwamnatinsa tare da rusa majalisar zartaswa da sauran hadimai.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Finti ya amince da mutane bakwai da aka zaɓa a matsayin sarakunan masarautu bakwai da ya kirkiro, ya faɗi sunayensu.
Hadimin gwamnatin Muhammadu Buhari, Babafemi Ojudu ya bayyana yadda suka tsorata Tinubu kan karbar mukamin minista a gwamnatin Umaru Musa Yar'adua.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ja kunnen masu rike da mukamai a gwamnatinsa kan shiga siyasa a shekarar 2025. Ya ce ba zai lamunci hakan ba.
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati. Gwamnan ya kuma raba wasu mukaman guda biyu a gwamnatinsa.
Nade-naden gwamnati
Samu kari