Yan bindiga
'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kewaye wani masallaci a jihar Zamfara sun sace masallata 40 ana tsaka da sallar Asuba. Sun tafi da masallata dajin Tsafe.
An bayyana fuskar Kachalla Babaro da ya kashe mutum 32 a wani hari da ya kai Malumfashi a jihar Katsina. Ya hallara zaman sulhu da aka yi da yan ta'adda a Faskari.
Jagoran ‘yan ta’adda da ake nema, Isiya Kwashen Garwa, ya amince da sulhu a Katsina; Sheikh Gumi ya ce zaman lafiya na dawowa, inda ya gargadi masu ta da rikici.
Kasurgumin dan bindiga, Ado Aliero ya bayyyana cewa yanzu kam za a zauna lafiya bayan zaman sulhu da aka yi a Faskari a Katsina. Aliero ya ce za a zauna lafiya.
Rahotannin da muke samu sun ce matashin dan sa-kai ya bude wuta a masallaci a ƙaramar Danko Wasagu da ke jihar Kebbi inda aka samu raunuka game da lamarin.
Rahotanni sun ce an gudanar da sulhu yau Lahadi 14 ga watan Satumbar 2025 a ƙaramar hukumar Faskari da ke jihar Katsina domin kare farmakin ’yan bindiga
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta kawo cikas a yunkurin gwamnatinsa na fara aikin titin da zai ci 18.9bn.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wani kauyen jihar Zamfara. 'Yan bindigan sun tattara mata da kananan yara zuwa daji yayin harin da su ka kai.
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan 'yan ta'adda a jihar Kogi. An kashe Kachalla Babangida bayan an bude wa 'yan bindiga wuta a wani dagi da suka buya.
Yan bindiga
Samu kari