Yan bindiga
Sanatan Borno ta Kudu, Mohammaed Ali Ndume ya caccaki masu rokon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kori hafsoshin tsaro duba da halin da ake ciki.
Binciken kwa-kwaf da aka gudanar ya karyata bidiyon da ake yadawa, inda ake ikirarin sojojin Najeriya na bai wa ’yan bindiga goyon baya a wani daji.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile harin 'yan bindiga a jihar Katsina. Sojojin sun samu nasarar ne tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro.
Sojojin Operation Fansan Yamma da jami’an tsaro sun yi nasarar dakile yunkurin ‘yan bindiga na kai hari wani kauyen karamar hukumar Malumfashi, an rasa rayuka.
Dakarun sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara. A yayin artabun an kashe 'yan bindiga masu yawa yayin da aka samu asarar rayukan wasu sojoji.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun kashe mutane tare da yin awon gaba da wasu masu yawa.
Wata kungiyar dattawan Arewa ta shawarci gwamnonin yankin da su bi hanyar sulhu domin kawo karshen matsalar rashin tsaro. Ta ce sulhu abu ne mai kyau.
Gwamna Nasir Idris zai kafa sansanin sojoji a karamar hukumar Augie, domin karfafa tsaro; ya kuma sanar da gyaran asibitin Augie don inganta kiwon lafiya.
Wani matashi ya yi tattaki daga Ikorodu zuwa Abakaliki na tsawon kwanaki 17 don godiya ga Gwamna Nwifuru, ya samu kyaututtuka ciki har da tallafin N10m.
Yan bindiga
Samu kari