Jihar Enugu
Kungiyar HURIWA ta musanta raɗe-raɗin dake yawo cewa tsohon gwamnan jihar Enugu ya yi layar zana don gudun EFCC ta nemi titsiye shi kan wasu kuɗi da ya wawure.
Janar Y. D Ahmed ya tabbatar da rashin ingancin takardar shaidar da Peter Mbah. Darekta Janar na NYSC ya yi wannan bayani lokacin da ake shirin rantsar da shi.
Sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawar Najeriya ya shiga tasku bayan labari ya bayyana na kama shi kan yunkurin cire kodar wani.
Gwamnan jihar Enugu ya dauki nauyin maniyyata Kiristoci 300 zuwa kasashen Jordan da Isra'ila masu tsarki don sauke farali a wannan shekara ta 2023 da ake ciki.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar matar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani. Mrs Jane Nnamani ta mutu a birnin Enugu bisa wata rashin lafiya.
Wani dan Najeriya ya wallafa wani faifan bidiyo tare da Wales Morgan in da yake nuna dankareren gidan da yake biyan kudin haya har 2m, ya koka kan rashin ruwa.
Kungiyar kabilar Ibo a Najeriya ta caccaki gwamnatin tarayya na yin burus wurin taimakon tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu da matarsa.
Kwanaki bayan an neme shi an rasa, an gano d'an takarar gwamna a inuwar APGA a jihar Enugu, Dons Ude, amma ya mutu, har yanzu 'yan sanda ba su ce komai ba.
Yanzu muke samun labarin yadda aka dakatar da tsohon gwamnan APC da kuma ministan Buhari mai ci a wannan makon bayan zarginsu da cinye dunduniyar jam'iyyar.
Jihar Enugu
Samu kari