Jihar Enugu
Mambobi 6 na majalisar dokokin jihar Enugu sun sauya sheka daga Labour Party da aka zaɓe su karkashinta, sun koma jam'iyyar PDP mai mulkin jihar kan wani daili.
Wasu ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mataimakiyar darakta da wani jami'in tsaro a asibitin jami'ar Najeriya da ke Enugu.
Kabilar Igbo sun bayyana dalilin da ya sa ba za su shiga zanga-zangar da ake yi a fadin Najeriya ba baki daya kan tsadar rayuwa inda suka ce an nuna musu wariya.
Wani mutum ya nuna kaduwarsa kan farashin da ya siya man fetur a jihar Enugu. Mutumin ya nuna shaida sannan ya bayyana sunan gidan man da ya siye shi kan haka.
Wasu miyagun 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yinawon gaba da wata gawa tare da masu rakiyarta a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya.
Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta ce wasu 'yan daba sun hargiza zaben cike gurbi da jami'an hukumar ke gudanarwa a jihar Enugu, an lalata kayayyakin zabe gaba daya.
Shugaban cocin Adoration Ministry da ke Enugu, Fasto Mbaka ya fito fili ya yi fallasa kan fastocin bogi masu shirya mu'ujizar karya da ba da bayanan karya.
Farfesa Anezionwu Okoro ya riga mu gidan gaskiya a jihar Enugu ya na da shekaru 94 a duniya, marigayin ya rasu a jiya Asabar 20 ga watan Janairu a Enugu.
Miyagun yan bindigan da suka sace basaraken kauyen Nkalagu Obukpa, sun sako shi bayan sun karbi makudan kudaden fansa da kayan abinci a hannun iyalansa.
Jihar Enugu
Samu kari