Zaben Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC d shirya amfani da hukumomi wajen hana su shiga zabe.
Kakaki a NDC ya maida wa Bashir Ahmad martani da ya ce 'dan takarar shugaban kasa zai canza jam'iyya. Theo Abu Agbada ya ce Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suna nan.
A labarin nan za a ji jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kwantar da hankulan 'yan jam'iyyar NDC game da kalubalen shari'a gabanin 2027.
A labarin nan, za a ji cewa NDC ta zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya da hana ta damar mika sunayen yan takararta a zaben 2027.
Jam'iyyar NDC a Bayelsa ta rasa wasu manyan jiga-jiganta, ciki har da ɗan takarar majalisar dokoki da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma, zuwa APC.
Hukumar INEC ta ɗaga ranar bai wa jam'iyyun siyasa lambar shiga manhajar gabatar da sunayen 'yan takara daga Juma'a zuwa Litinin, 29 ga Yunin shekarar 2026.
Wani jigon APC, Taoreed Mustapha, ya ce wasu da ake zargin 'yan daba na siyasa sun harbe shi a Osogbo bayan ya sauya sheka daga jam'iyyar Accord zuwa APC.
Hukumar INEC ta bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fitar da kudin da aka ware domin shirye babban zaben 2027 ba, amma an fara shirye-shirye.
Hukumar INEC na shirin cire NDC daga rajistar jam’iyyun siyasa bayan kotu ta soke hukuncin da ya umarci hukumar ta yi wa jam'iyyar rajista gabanin 2026.
Zaben Najeriya
Samu kari