Jihar Edo
Yayin da zaben gwamna na 2024 a jihar Edo ke kara gabatowa, jam’iyyar PDP ta tsayar da Asue Ighodalo a matsayin dan takararta domin karawa da wasu.
Asue Ighodalo ya ce Edo PDP za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a lokacin da gwamnatin tarayya da ‘yan sanda suka saki 'yan jam’iyyar da aka tsare.
Jigon APC a jihar Edo ya ce za su yi nasara a zabe mai zuwa a jihar Edo duk da wahalar rayuwa da ake fama. Ya ce ba Bola Tinubu ba ne ya kawo wahalar rayuwa Najeriya
Jihar Edo dai na da gwamnoni 10 na soja da na farar hula tun daga shekarar 1991 har zuwa lokacin da aka yi zaben dimokuradiyya a 1999. Mun tattaro jerin gwamnonin.
Dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo na daga cikin manyan 'yan takarar gwamna a zaben na ranar Asabar, 21 ga watan Satumba.
Dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar Action Alliance (AA) a zaben jihar Edo, ya janye daga yin takara. Ya marawa dan takarar APC baya.
Ana shirin gudanar da zaben jihar Edo, an kammala kamfen a duka bangarorin jam'iyyu inda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Abdullahi Ganduje suka halarta.
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa zaben gwamnan jihar da ke tafe a mutu ko a yi rai ne. Ya bukaci jama'a su fito su zabi jam'iyyar PDP.
Yayin da ake ta shirin gudanar da zaben jihar Edo, tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya roki basarake a jihar kan kura-kurai da ya tafka lokacin yana gwamna.
Jihar Edo
Samu kari