Jihar Edo
Shugaban kungiyar NLC a Edo, Odion Olaye ya sake rura wutar rikici yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar 2024 da muke ciki.
Kotun daukaka ta zartar da hukunci kan karar da ke neman soke tikitin takarar gwamna na Barista Olumide Akpata karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party.
Yayin da ake shirin zaben jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya ki amincewa da sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya kan zaben da ke tafe nan da kwanaki tara.
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi zargin cewa ana shirin cafke magoya bayan jam'iyyar PDP gabanin zaben gwamnan jihar da ke tafe nan da kwanaki masu zuwa.
Wasu jihohi a Najeriya sun dauki matakin dage ranakun da dalibai za su koma makarantu. Wasu daga ciki sun dauki matakin ne saboda tsadar fetur da wasu dalilan.
Kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Edo ya fara zargin Gwamna Godwin Obaseki da shirya wata manaƙisa da nufin ruguza zaɓen da za a yi a jihar a watan nan.
Ana shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya yi babban rashi bayan hadimansa guda hudu sun yi murabus tare da watsar da PDP.
Tsohon dan majalisar dokokin jihar Edo, Honarabul Emmanuel Agbaje ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP. Ya sauya shekar ne bayan ya fice daga jam'iyyar APC.
Dan takarar gwamnan APC a jihar Edo, Monday Okpebholo ya tafka kuskure yayin kamfen da aka gudanar a karamar hukumar Ovia ta Arewa ana daf da zabe.
Jihar Edo
Samu kari