Dollar zuwa Naira
An tsare wasu manyan jami'ai biyu na kamfanin Binance a Najeriya, a cewar Financial Times (FT), wata kafar yada labaran kasuwanci da ke Birtaniya.
Babban lauya a Najeriya, Mike Ozekhome, ya yi hasashen cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, darajar Naira sai ta fadi kasa zuwa N4000/$1 kafin karshen 2024.
Bayan koken koken jama'a, an ji labari CBN ya cigaba da saida Daloli ga ‘yan kasuwar canji. Idan Dala ta fara wadatuwa a bayan fage, farashin Naira zai tashi.
Dabaru sun taimaka Naira ta danne dalar Amurka a kasuwar canji. An ce tun da dai Dalar Amurkar tana fadi ne a kan kudin Najeriya, ya kamata farashin kaya su sauko.
‘Yan kasuwar canji musamman daga Arewa sun tsorata daga sababbin ka’idojin CBN. Wasu sun ce farashin Dalar Amurka za ta cigaba da hawa ne a maimakon ta sauka.
Bayanai sun fito yayin da Bola Tinubu ya zauna da Aliko Dangote da sauran ‘yan kasuwa. Tinubu ya yi zama da manyan ‘yan kasuwan ne domin gyara tattalin arziki.
An ruwaito yadda dukiyar attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika ta ragu bayan da aka samu ragi a darajar Naira a kasuwar duniya a cikin kwanakin nan.
A game da tashin Dala, wani masani ya haska kuskuren gwamnatin Bola Tinubu. IMF ta ce $1 za ta haura N2000 a 2024, masanin ya taba ba Muhammadu Buhari shawara.
Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta kama wasu masu gudanar da canjin kudi a shahararriyar kasuwar canji ta WAPA da ke jihar Kano.
Dollar zuwa Naira
Samu kari