Kotun Kostamare
Jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewa sabon kwafin takardar CTC na hukuncin kotun daukaka kara kan shari'ar Kano kuskure ne na rubutu da kotu za ta gyara.
Magidancin ya shaidawa kotun cewa yana dukan matar da yaran ne kawai idan suka aikata laifi, kuma yana yin hakan don gyara masu tarbiya. Alkalin ya ba shi shawara.
Mai shari’a Hakeem Oshodi na wata babbar kotu a Legas, ya gargadi jama’a da su daina barin layoyi a kotunsa domin ba sa aiki kuma. Ya yi gargadin yayin zaman kotu.
Wata kotun majistare mai zama a birnin Port Harcourt na jihar Rivers, ta tura wasu mutum biyu zuwa gidan gyaran hali bisa cin zarafin wani tsohon kan satar mazakuta.
Dan addinin gargajiya, Abdulazeez Adegbola, wanda ya ƙona Alkur'ani aka maka shi a Kotu ya roki ɗaukacin al'ummar Musulmai su yafe masa abinda ya yi.
Yan Najeriya sun fito dandalin soshiyal midiya inda suka tofa albarkacin bakunansu a kan hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige Abba gida-gida daga gwamna.
An ga abin mamaki wajen shari'ar zaben gwamnan Nasarawa da aka yi satar waya. Tsohon Minista Maku ya shiga kotun zaben Gwamna, ya fito babu wayar salularsa.
Babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature, ya yi watsi da rahotannin da ke sanar da ranar da kotun daukaka kara zata yanke hukunci a shari'ar zabe.
Kotun daukaka kara za ta zartar da hukunci kan makomar Babajide Sanwo-Olu a matsayin gwamnan jihar Lagas a yau, a shari’ar da ke neman a tsige shi.
Kotun Kostamare
Samu kari