Jihar Borno
Sanata Ali Ndume ya nuna alhininsa kan ambaliyar ruwan da ta auku a birnin Maiduguri na jihar Borno. Sanatan ya bukaci gwamnatin tarayya ta kai dauki a jihar.
Mahukuntan jami'ar Borno (UNIMAID) sun dauki matakin rufe jami'ar har sai abin da hali ya yi sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a birnin Maidiguri na jihar.
A wannan labarin, daurarrun da ba a kai ga sanin adadinsu ba sun samu damar tserewa daga kurkukun da aka ajiye su bisa laifuffuka daban-daban a Borno.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar NEMA ta gaggauta kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Maiduduri, yana mai jajantawa gwamnatin Borno.
Ambaliyar ruwa ta rusa gidan dabbobi da ke Maiduguri a jihar Borno. Dabbobi kamar kada da macizai sun shiga gari ta cikin ruwa. Kashi 80 na dabbobi sun mutu.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya umarce shi da ya bar Abuja zuwa birnin Maiduguri domin duba ambaliyar da ta faru.
Ambaliyar ruwa ta wargaza makabarta a Maiduguri. Makabartar Kiristoci da ruwan ya rusa tana GRA. An shiga fargaba kan barkewar cututtuka daga makabartar.
Gwamnatin jihar Borno ta bukaci mazauna Maiduguri musamman kusa da kogi da su gaggauta barin yankin domin kare kansu daga ambaliyar ruwa bayan ballewar Alau.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya aika sakon jajantawa ga gwamnati da al'ummar jihar Borno kan iftila'in ambaliyar ruwa da ya mamaye Maiduguri da kewaye.
Jihar Borno
Samu kari