Jihar Borno
Yayin da al'umma ke kokawa kan karin farashin man fetur a Najeriya, Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya roki alfarma wurin Bola Tinubu kan halin kunci da ake ciki.
Gwamnatin Borno ta yi gyara kan adadin tubabbun yan Boko Haram da su ka tsere daga wurin da ake ba basu horo. Gwamnatin ta ce mutum shida ne su ka gudu.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi. Gwamna Zulum ya sa lokacin fara biya.
A wannan labarin, Sanata Ali Ndume ya bayyana ainihin abin da ya faru kan labarin da ake yadawa na cewa yan kungiyar Boko Haram sun kai masa hari.
Yan ta'addar Boko Haram da suka tuba ana ba su horo domin taimakon sojoji da bayanai sun tsere da makamai, suna barazanar kai hare hare kan al'umma.
Mayakan Boko Haram sun kai wani mummunan hari kan rundunar sojoji da daren ranar Litinin 7 ga watan Oktoban 2024 inda aka rasa rayuka da dama yayin harin.
Rabaran Alaku Vincent, sanannen malamin addinin Kirista a Maiduguri, babban birnin Borno, ya mutu a ranar Lahadin da ta gabata, yayin bikin sadaukarwar yara.
Gwamnatin jihar Borno ta hannun ma'aikatar lafiya ta sanar da ɓarkewar cutar kwalara a wasu ƙananan hukumomi sakamakon ambaliyar ruwan da ta faru.
A wanna rahoton, gwamna Babagana Umara Zulum ya fusata da mutanen da su ka gina muhallansu a gabar ruwa a jihar Borno wanda ya ta'azzara ambaliya.
Jihar Borno
Samu kari