Aikin Hajji
Sanata Ali Ndume ya yi Allah wadai da karin kudin kujerar aikin hajji inda ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya biya cikon kudin ga maniyyata domin rage musu wahala.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sanar da bayar da tallafin N500,000 ga kowane maniyyaci da ke shirin zuwa aikin hajjin 2024 a jihar, bayan karin kudin Hajj.
Rahotanni daga wasu jihohin Najeriya sun nuna yadɗa maniyyata ke zuwa neman a dawo masu da kuɗaɗensu bayan NAHCON ta sanar da ƙarin N1.9m a kowace kujera.
Bayan shekara 33, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya aza harsashin ginin sansanin alhazai wa al'ummar Musulmi, wanda shi ne na farko tun bayan kafa jihar.
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da yin karin kudin zuwa aikin hajjin bana na shekarar 2024. A yanzu maniyyata za su kara M1.9m domin zuwa Saudiyya.
Wani rahoto da ke fitowa daga Saudiyya ya bayyana cewa, Saudiyya ta haramtawa maniyyata yin Umrah sau biyu a cikin watan Ramadana saboda wasu dalibai.
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa, a matsayin jagora kuma Amirul Hajj na aikin Hajjin 2024.
Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci saka tallafi a harkar jigilar maniyya aikin hajji saboda muhimmancinsa ga addinin Muslunci da kuma tsadar rayuwa da ake ciki.
Hukumar jin dadin Alhazai ta koka yayin da alamu suka nuna ba za ta iya cike gurbin yawan kujeru da aka ba ta ba na aikin hajji a wannan shekara.
Aikin Hajji
Samu kari