Aikin Hajji
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da amincewa da karin wa'adin lokacin biyan kudin aikin Hajjin 2024. Hukumar ta yi hakan ne bayan wa'adin farko ya kare.
Hukumar aikin Hajji ta jihar Zamfara ta fara mayar da naira miliyan 747 ga maniyyata 504 da suka fara tara kudin tun daga 2019 zuwa 2023. Shugaban hukumar, Musa.
Hukumar jin dadin alhazai, NAHCON ta koka kan yadda ta gaza cike gurbin kujerun aikin hajjin bana guda dubu 95 saboda wasu dalilai da suka shafi dala.
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da jin daɗin alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da cewa Musulmai za su biya N4.5m na hajjin bana 2024.
Gwamnatin jihar Filato, ta kafa wani kwamiti da zai binciki jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar, bisa zargin karkatar da naira miliyan 200 na wasu maniyyata.
Hukumomin Saudiyya sun soke bizar yan Najeriya su 264 da suka tafi kasar mai tsarki don yin Umrah da wasu hidimomin. Da isarsu aka sanar da su cewa a soke bizar.
Shugaban kasa Tinubu zai yi Umrah a kasar Saudiyya bayan halartar wani taron zuba hannun jari da aka yi kan matatun man Najeriya da yadda za su gyaru.
Kungiyar AHOUN ta kamfanoni masu kula da zirga-zirgar zuwa aikin Hajji, ta yi nuni da cewa za a iya samun ƙarin kuɗin zuwa aikin Hajji a shekarar 2024.
Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce kasar Saudiyya ta ba maniyyatan kasar nan mako 3 su fara biyan kafin alkalami na kudaden kujerar Aikin Hajjin 2024.
Aikin Hajji
Samu kari