Abun Al Ajabi
Rundunar 'yan sanda ta gano wasu fursunoni 300 da ke zaman wakafi a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano, ba tare da wata takarda ta bayanin shari’arsu ba.
Wata matashiyar budurwa ta yada bidiyo don nunawa duniya gidan da ta siya tana mai shekaru 26 a duniya. Ta cika da murna, tana mai cewa da kudinta ta soiya gidan.
An rahoto cewa wani ‘dan Najeriya da ya mallaki gida ya kara kudin hayar gidan da ya gina shekaru 30 da suka wuce kan hujjar cewa an samu kari a kudin siminti.
Wani ‘dan Najeriya ya zolayi mutane a titi ta hanyar ajiye kudinsa a kasa tare da daukar bidiyon abin da suka yi da suka ga kudi. An gano gaskiyar wasu mabarata.
Facebook, Messenger da Instagram na kamfanin Meta sun dauke a duk duniya, wanda ya bar dubban daruruwan masu amfani da su cikin yanayi na rashin abin yi.
Wata matashiya ‘yar Najeriya ta haddasa cece-kuce bayan ta yada bidiyon adaidaita sahun da ta shiga. Keken na dauke da talbijin, fanka da lallausar kujera.
Betty Akeredolu, Matar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta caccaki surukarta, Funke Akeredolu Aruna bayan ta nuna goyon baya ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Wani matashi 'dan kungiyar JIBWIS daga jihar Katsina, Salihu Abdulhadi Kankia ya tsinci jaka dauke da naira miliyan 100 sannan ya mayarwa mai ita.
Hukumar NYSC da ‘yan Najeriya sun jinjinawa wata ‘yar bautar kasa, Adedeji Taofeekat Adebimpe, wacce ta tsinci wayar iPhone 13 Pro Max da ta bata sannan ta mayar.
Abun Al Ajabi
Samu kari