Abuja
Shugaba BolaTinubu ya sake magana kan halin kunci inda ya ce cire tallafin mai ba abu ne mai sauki ba, amma wajibi ne domin ceto tattalin arzikin Najeriya.
Majalisar Dattawa ta amince da kasafin Naira biliyan 140 ga hukumar NCDC don manyan ayyuka da gudanarwa a Abuja da jihohi shida na Arewa ta Tsakiya.
Gwamnatin tarayya ta soke faretin ranar yancin kan Najeriya ta shekara 65, sakataren gwamnatin taraya, Goerge Akume ya ce lokaci ne na tunani da kishin kasa.
Bayan kisan gilla kan yar jarida a Abuja, Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da hallaka matashiyar inda ya bukaci yin binciken gaggawa domin gano maharan.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ba gwamnonin Arewa shawara kan matsalar rashin tsaro. Gwamnan ya bukaci su tashi tsaye wajen magance matsalar.
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tare da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai sun samu damar halartar bikin dan Rotimi Amaechi a cikin cocin Abuja.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya gana da shugaban jamiyyar hadaka ta ADC a Abuja. Ya gana da David Mark ne bayan taron manyan ADC.
A labarin nan, za a ji cewa wani lauya mai fafutuka, Ademiluyi ya shigar da kara a gaban wata kotun Abuja yana neman bayani a kan kudin da aka tara wa Remi Tinubu.
NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai tsanani da tsawa a jihohi da dama na Najeriya a ranar Alhamis 25 ga Satumba, tare da yin kira ga jama'a da su yi taka-tsantsan.
Abuja
Samu kari