Abuja
Majalisar Shari’a ta ƙasa ta bukaci Bola Tinubu ya sake nazarin nadin Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban INEC kan zargin rubuta takarda da ta soki Musulmai.
Tsagin PDP na Abdulrahman ya zabi Mao Ohabunwa a matsayin sabon shugaban kwamitin amintattu domin dawo da adalci, gaskiya, da amincewar jama’a a cikin jam’iyyar.
A labarin nan, za a ji yadda Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB ya shaidawa kotu cewa baki daya shari'ar da ake yi da shi ba ta bisa tsarin adalci.
Kamfanin samar da wutar lantarki a Abuja (AEDC) ya fara sallamar ma’aikata kusan 800 bayan watanni na sake tsari a cikin gida wanda aka yi niyyar korar 1,800.
Ministan noma na kasa, Sanata Abubakar Kyari ya ce gwamnatin tarayya na fatan sauke farashin taki da sauran kayan shuka a Najeriya domin bunkaa noma.
Hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta ce za ta kaddamar da taswirar jiragen kasa da za ta ba kowace jihar damar amfana da layin dogo a Najeriya.
A labarin nan, za a ji cewa Dave Umahi, Ministan ayyuka na Najeriya ya sanar da cewa majalisar zartarwa ta amince da fitar da sama da N400bn domin wasu ayyuka.
Jakadan Isra'ila a Najeriya, Micheal Freeman ya bukaci 'yan Najeriya su hada kai su zauna lafiya domin samun cigaba. Malaman Musulunci da Kiristoci sun yi martani.
Rundunar ‘Yan sanda ta janye karar Naira miliyan 400 da ta shigar kan tsohon Sanata Andy Uba da abokinsa, bayan sulhu tsakanin ɓangarorin da ke rikici.
Abuja
Samu kari