JAMB
Kotun majistare da ke Kado a birnin Abuja ta daure ma'aikacin JAMB, Emmanuel Odey kan satar kwamfuta da ta kai Naira dubu 350 don biyan kudin haya na gidansa.
Musa Isa Salmanu, mahaifin Isa Salmanu da ya samu sakamako mafi kyau (A1) guda 9 a dukkan darusan da ya dauka ya bayyana irin gudumawar da ya bayar ga yaron.
Mmesoma Ejike, dalibar nan da hukumar JAMB ta zarga da kirkirar sakamakon jarrabawarta na UTME, ta ba hukumar shirya jarrabawar hakuri a kan abun da ta aikata.
Wani matashi ya wallafa wani faifan bidiyo da aka gano wani dalibi hannunsa na rawa ya na kokarin duba sakamakon jarrabawar 'JAMB', a karshe ya samu maki 158.
Yau muke samun labarin yadda gwamnan jihar Anambra ya ba da umarnin dalibar nan da ta kara sakamakon JAMB a zauna da ita don sanin inda ake da matsala da tushe.
Mmesoma Ejikeme ta yi kuka a cikin wani bidiyo wanda ya nuna hirar da ta yi a waya, kan kunyar da ta ke ji a dalilin sauya sakamakon jarabawarta na JAMB/UTME.
Attajirin dan Najeriya ya bayyana cewa yana nan a kan bakarsa na daukar nauyin karatun Mmesoma duk da ta kirkiri sakamakon JAMB dinta. Ya ce zai bata shawara.
Bayan gano gaskiya da kuma gano yadda wata daliba ta jirkita sakamakon jarrabawarta na JAMB, mahaifinta ya fito ya bayyana gaskiya, ya nemi afuwar hukumar.
Kamfanin motoci na Innoson ya janye tallafin karatu da ya baiwa Joy Mmesoma Ejikeme bayan bincike ya tabbatar da sakamakon jarrabawarta na UTME na bogi ne.
JAMB
Samu kari