Ilorin
Wata matar aure mai suna Aminar ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta bisa rashin nuna soyayya, kulawa da ɗaukar ɗawainiyar iyalansa a Ilorin jihar Kwara.
Yan sanda sun kama wasu dalibai hudu na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) mai suna Malete da suka lakadawa wani abokin karatunsu dukan tsiya har lahira.
Wata matar aure mai suna Ramat Joke ta roki wata kotu da ke Ilorin, da ta datse igiyar aurenta a kan cewa mijinta, Habeeb Atanda ya koma mashayin kwaya.
Wata dalibar aji hudu a jami’ar jihar Kwara, Malete da ke karamar hukumar Moro, mai suna Rashidat Shittu, ta dauki ranta da kanta saboda ta samu matsala a karatunta.
A ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu ya kamata a daura auren mataimakin Bursar na jami'ar jihar Kwara, Ayuba Olaitan, wanda ya rasu yayin kallon wasan Najeriya.
Mai martaba Sarkin Ilorin ya ce tun da aka kafa hukumar EFCC bai taɓa zuwa ya nemi a taimaka a kyale wani da hukumar ke tuhuma da aikata wasu laifuka ba
Dan addinin gargajiya, Abdulazeez Adegbola, wanda ya ƙona Alkur'ani aka maka shi a Kotu ya roki ɗaukacin al'ummar Musulmai su yafe masa abinda ya yi.
‘Yan fashi sun raba wani mutum da kudinsa bayan ya fito daga cikin banki. Abin da ya bada mamaki shi ne wadanda su ka yi fashin sun zo da shihar 'yan sanda.
Wata kotu da ke zamanta a Ilorin babban birnin jihar Kwara ta tura wata shugabar masu addinan gargajiya Iya Osun gidan yarin saboda cin mutuncin malamin addini.
Ilorin
Samu kari