An Zabi Sabon Shugaban ADC a Kano bayan Shigar Kwankwaso, Mutane 27 Sun Samu Mukami
- Jam'iyyar ADC ta zabi sababbin shugabanni a matakin jihar Kano yayin da take shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027 mai zuwa
- Abdullahi Maikano Tarauni, wanda ake ganin yana da kusanci da Rabiu Kwankwaso a siyasa, ya zama sabon shugaban ADC na Kano
- An kuma zabi sauran mambobin kwamitin gudanarwa na ADC (NWC) reshen jihar a taron da ya gudana ranar Lahadi da ta gabata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Jam’iyyar ADC ta zabi Abdullahi Maikano Tarauni, wanda ake ganin na kusa da Rabiu Musa Kwankwaso ne, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar a jihar Kano.
Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso ya sauya sheka daga NNPP zuwa jam'iyyar ADC.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta tattaro cewa an gudanar da zaben ne a taron jam’iyyar na jiha da aka yi ranar Lahadi, inda aka kuma fitar da sababbin shugabannin jam’iyyar a matakin jiha.
Jerin sabqbbin shugabannin ADC a Kano
Haka zalika an zabi Hon. Ali Datti Yako daga Kiru a matsayin mataimakin shugaban jam'iyya na jihar Kano. Sauran wadanda suka shiga kwamitin gudanarwa na ADC jihar sun hada da:
1. Hon. Ali Shettima (Nassarawa) – mataimaki na farko
2. Hon. Bashir Kofa (Bebeji) – mataimaki na biyu
3. Hon. Bello Yandadi (Ghari) – mataimaki na uku
4. Dr. Bala Muhammad Inuwa (Takai) – sakataren ADC
5. Dr. Haruna Rogo (Rogo) – mataimakin sakatare
6. Hon. Abba Muktar (Danbatta) – ma’aji
7. Hon. Balarabe Sarki (Bichi) – mataimakin ma’aji
8. Farfesa Salis Muhammad – sakataren kudi
9. Hon. Nura Makoda – mataimakin sakataren kudi
10. Hon. Shehu Kabo – sakataren yada labarai
11. Hon. Magaji Ya’u Indabawa (Kano Municipal) – mataimakin sakataren kudi
12. Barista Muhammad Yahaya (Kura) – mai ba da shawara kan shari’a
13. Barista Tahir Ibrahim Yakasai – mataimakin mai ba da shawara kan shari'a
14. Hon. Yusuf Bature (Nassarawa) – sakataren walwala
15. Hon. Kabiru Garba Abba (Sumaila) – mataimakin sakataren walwala
16. Hon. Sunusi Surajo (Madobi) – sakataren tsare-tsare
17. Hon. Alu Karaye (Karaye) – mataimakin sakataren tsare-tsare
18. Hon. Sa’adu Zangon Mata (Dawakin Tofa) – Audita Janar
19. Dr. Shehu Ibrahim Bawa (Tarauni) – mataimakin Audita Janar
20. Hon. Ahmad Maikoriya (Dawakin Kudu) – shugaban masu bukata ta musamman
21. Hon. Farida Kamba (Ungoggo) – shugabar mata
22. Hon. Hauwa Awaisu (Shanono) – mataimakiyar shugabar mata
23. Hon. Sunusi Oscar (Fagge) – shugaban matasa
24. Hon. Abba Abdulhamid (Kumbotso) – mataimakin shugaban matasa
25. Hon. Mustapha Bala Getso (Gwarzo) – mai tsawatarwa
26. Hon. Bashir Tijjani Maisango (Nassarawa) – mataimakin mai tsawatarwa.

Source: Facebook
ADC na shirye-shiryen zaben 2027
Kwankwaso ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook, inda aka gan shi ya halarci taron zaben shugabannin ADC.
Zaben wadannan sababbin shugabanni na ADC na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Kano ke kara zafi, musamman yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027.
Sabon bangare ya bulla a jam'iyyar ADC
A wani rahoton, kun ji cewa rikicin jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ya kara tsananta bayan bullowar sabon bangare ana shirin zaben 2027.
Sabon tsagin ya bayyana cewa ba ya goyon bayan bangaren David Mark ko na Nafiu Bala, yana mai cewa yana wakiltar sahihan shugabannin jam’iyyar ADC.
Jagoran sabon bangaren, Don Norman Obinna, ya yi ikirarin cewa su ne halastattun mambobin kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka zaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


