"APC Ta Yi Abin Kunya": Diyar Buba Ta Fadi Yadda Gwamnatocin Tinubu da Buhari Suka Gaza

"APC Ta Yi Abin Kunya": Diyar Buba Ta Fadi Yadda Gwamnatocin Tinubu da Buhari Suka Gaza

  • 'Diyar fitaccen 'dan siyasa Zainab Buba Galadima ta bayyana nadamar kasancewarta daya daga cikin 'yan APC da suka yi wa jam'itta fafutuka
  • Ta bayyana cewa jam'iyyar da ta yi zaton za ta fitar da 'yan Najeriya daga mawuyacin hali ta gaza cimma manufofin da aka kafa jam'iyyar a kai
  • Zaina ta kwatanta salon mulkin APC a karkashin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – 'Diyar fitaccen 'dan siyasa, Zainab Buba Galadima, ta bayyana cewa tana jin kunya da nadama kan kasancewarta a jam’iyyar APC.

Ta bayyana cewa ta ji kunya sosai bayan ta tallata gwamnatocin da syka gaza cika alkawuran da ta dauka wa ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya nemi babbar Alkali Najeriya ta sauya mai kula da shari'arsa, ya bayyana dalili

Zainab Buba Galadima ta ce APC ta gaza
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zainab Buba Galadima a hagunsa Hoto; Bayo Onanuga/Zaynab Galadima
Source: Facebook

Zainab Buba Galadima ta bayyana haka ne ta cikin wata hira da Jaridar The Cable ta wallafa bidiyonsa a shafinta na X.

'Diyar Galadima ta magantu kan mulkin APC

A cikin hirar Zainab ta ce tana cikin wadanda suka kafa APC daga tsohuwar jam’iyyar CPC, inda ta bayyana cewa sun shiga jam’iyyar ne bisa imanin cewa marigayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kawo sauyi mai ma’ana tare da saukaka rayuwar talakawa.

Sai dai ta bayyana cewa hakan bai tabbata ba, tana mai zargin Buhari da mutanen da ke kewaye da shi da gaza cika wannan alkawari da aka tallata APC a kansa.

Ta ce:

“Eh, ya (Buhari) gaza, shi da mutanen da ke tare da shi, sun gaza matuka."

APC ta gaza cika alkawuranta - 'Diyar Galadima

Zainab ta kara da cewa tana jin kunya da takaici kan alakarta da APC, tare da bayyana cewa ba za ta iya alfahari da kasancewarta a cikin jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

'Sun aikata zunubi': Gwamnatin tarayya ta tura mutane 386 gidan yari a Abuja

A kalamanta:

“Na ji kunya. Na yi nadama. Ba zan iya tafiya ina daga kai ina cewa ina cikin wannan kungiya ba."

Ta kuma kwatanta ficewarta daga jam’iyyar da fita daga aure mai cike da matsaloli, inda ta ce mutum kan jure abubuwa da dama har zuwa lokacin da zai yanke shawarar barin wannan hali gaba daya.

Sai dai ta bayyana cewa har yanzu tana girmama wasu nagartattun mutane da ke cikin jam’iyyar, domin akwai nagari da marasa nagarta a ko’ina.

'Diyar Buba Galadima ta ce shugabannin APC sun gaza
Shugaban kasa Bola Tinubu da tsohon shugaba marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Zainab ta bayyana cewa ana ci gaba da tuntubarta daga matakai daban-daban na jam’iyyar, daga matakin mazaba har zuwa na kasa, inda ake tambayarta dalilin ficewarta.

Ta ce har ta kai ziyara gidan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, inda ta hadu da wasu sanatoci masu ci daga APC, wadanda suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda al’amura ke tafiya a cikin jam’iyyar.

Ta nanata cewa dukkanin shugabannin da APC ta samar sun gaza daga kan Muhammadu Buhari zuwa Tinubu, tare da jaddada cewa lamura sun fi tabarbarewa a yanzu.

Kara karanta wannan

"Ba mu bukatarka," Gwamna Bala ya samu gagarumar matsala a shirinsa na komawa APC

Diyar Buba ta magantu kan APC

A baya, mun wallafa cewa Zainab Buba Galadima, ɗiyar fitaccen ɗan siyasa ta ce ƴan Najeriya sun janye goyon baya ga shugaba Bola Tinubu saboda halin da suke ciki da ake zargin gwamnati ta yi biris da su.

Ta zargi APC da cin amanar jama’a duk da irin ƙoƙarin da aka yi wajen kawo ta mulki da yi wa mutane dadin baki, sannan ta yi gargadin cewa dole jama’a su tashi tsaye kafin zaɓen 2027 domin kare mutuncinsu.

Zainab Buba Galadima ta bayyana cewa duk da irin ƙarfi da iko da jam’iyyar APC ke da shi, amma talakawan Najeriya ba za su sake amincewa da su ballantana su sake zaben jam'iyyar a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng