2027: Nafiu Bala Ya Kawo Tsarin Hana Atiku, Obi da Kwankwaso Takara a ADC

2027: Nafiu Bala Ya Kawo Tsarin Hana Atiku, Obi da Kwankwaso Takara a ADC

  • Nafiu Bala da ke ikirarin shi ne sahihin shugaban jam'iyyar adawa ta ADC ya yi magana kan tsare-tsaren da za su kawo domin zaben 2027
  • Ya yi magana kan shekarun wanda za su tsayar takarar shugaban kasa, inda ya ambaci shekarun da duk wanda ya wuce ba za su ba shi dama ba
  • Nafiu Bala yi bayani kan korafin da ake game da ikirarin cewa shi ne shugaban jam'iyyar da kuma zargin cewa APC ce ta ke amfani da shi a ADC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Nafi’u Bala da ke ikirarin zama shugaban wani ɓangare na jam’iyyar ADC ya jaddada cewa ba za a iya kwace shugabancinsa ta hanyoyin da ba su dace ba.

A wani bayani da ya yi, Nafiu Bala ya yi gargadin cewa dole ne a bi ƙa’idoji da matakan da suka kamata wajen tantance mambobinsu kuma ba APC yake yi wa aiki ba.

Kara karanta wannan

Putin ya sanar da dakatar da yakin da Rasha ke gwabzawa da Ukraine

Nafiu Bala a wani taron ADC
Nafiu Bala da ke ikirarin zama shugaban ADC a wani taro. Hoto: Nafiu Bala
Source: Facebook

Bala da ke ikirarin jagorancin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa yayin da ake zarge-zarge game da shi.

Shirin hana Atiku, Obi takara a ADC

Game da shugabancin ADC, Nafiu Bala ya ce dole ne a bi kundin tsarin mulkin jam’iyyar yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa ba za a ba kowa matsayi ba tare da bin doka ba.

Ya bayyana cewa a karkashin shugabancinsa, duk wanda ya haura shekaru 55 ba zai cancanci tsayawa takara a ADC ba.

Rahotanni sun nuna cewa ya fadi haka ne yayin da ya ke cewa za su ba matasa damar shiga siyasa da tsayawa takara a zaben 2027.

An fassara wannan magana da ya yi da shirin hana Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso takara kasancewar sun haura shekara 55.

A yanzu haka dai Atiku Abubakar na da shekara 79, Peter Obi na da shekara 64 yayin da Sanata Rabiu Kwankwaso ke da shekara 69.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta saki bidiyon mutanen da ta kama, mata sun roki Tinubu, Shettima

Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi a zanga-zangar ADC
Yadda Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi da manyan ADC suka yi zanga-zanga a Abuja. Hoto: Rabiu Kwankwaso
Source: Facebook

Magana kan shugabancin jam'iyyar ADC

A cikin bayanan shi, Nafiu Bala ya ce wasu mutane da ba su ma yi rajista a jam’iyyar ba suna shiga cikinta suna ikirarin shugabancinta.

Daily Trust ta rahoto ya yi karin bayani game da sharudan kundin tsarin mulkin jam’iyyar dangane da zama mamba da cancantar shugabanci.

Nafiu Bala ya ce kundin tsarin mulkinmu ya fayyace yadda ake zama mamba a ADC, inda ya ce mutum ba zai yanki kati kawai a wani taro ba sannan a ayyana shi a matsayin shugaba.

Bala ya kuma yi bayani kan halartar wani taron jam’iyya da ya samu halartar manyan ’yan siyasa, yana cewa bai kamata a ɗauki halartarsa a matsayin goyon baya ga wani ɓangare na shugabancin ADC ba.

Kiran Kwankwaso ga Nafiu Bala

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Kwankwaso da ya shiga ADC ya yi kira da Nafiu Bala ya daina ikirarin shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ba labarin Kwankwaso, Atiku da Tinubu: Malami ya yi hasashen mai nasara a 2027

Ya bayyana haka ne bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana jiran Nafiu Bala domin su tattauna amma bai amsa gayyatar da ya masa ba.

Kwankwaso ya yi kira ga mai martaba Sarkin Gombe, 'yan siyasar jihar da malamai da su ja kunnen Nafiu game da rusa jam'iyyar ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng