Ba Labarin Kwankwaso, Atiku da Tinubu: Malami Ya Yi Hasashen Mai Nasara a 2027

Ba Labarin Kwankwaso, Atiku da Tinubu: Malami Ya Yi Hasashen Mai Nasara a 2027

  • Wani malamin addinin Kirista a Najeriya ya yi hasashe game da zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara
  • Faston ya yi hasashen da ya ba mutane mamaki saboda ya nuna shugaba Bola Tinubu bai da nasara a zaben
  • Malamin ya gargadi cewa duk wani yunkurin magudin zabe zai iya haifar da abubuwan da ba a taba gani ba a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia - Wani malamin addini daga Abia, Solomon Emeka Eliyah, ya yi hasashe game da zaben shugaban kasa a 2027.

Malamin ya bayyana cewa dan siyasa Peter Obi na iya zama shugaban Najeriya a zaben 2027 idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya.

An yi hasashen wanda zai yi nasara a zaben 2027
Sanata Rabiu Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi.
Source: Facebook

Fasto ya yi hasashen zaben 2027

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, faston ya ce yana ganin za a samu sauyin mulki a zaben mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Ba tabbas": Malamin addini ya yi hasashe kan tazarcen Tinubu a 2027

Ya kara da cewa zaben 2027 zai fi karfin siyasar jam’iyyar APC, yana mai cewa babbar matsalar jam’iyyar ita ce Peter Obi saboda shi na al'umma ne.

Ya ce:

“Allah yana gaya mani wani abu da ban taba yarda da shi ba a baya, amma yanzu na gaskata saboda maganar Allah ce.
“A 2027, Peter Obi yana kan gaba. Ba wai kawai yana kan gaba ba, shi ne tsarin shugabanci da aka riga aka amince da shi a sama, amma ana kai masa hare-hare a ko’ina."

- Solomon Emeka Eliyah

Fasto ya 'gano' wanda zai yi nasara a zaben 2027
Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga, Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Gargadin fasto kan magudin zabe a 2027

Faston ya gargadi cewa duk wani kuskure na magudin zabe zai iya haifar da abubuwan da ba a taba gani ba a Najeriya.

Ya ce ana kokarin hana Peter Obi cimma burinsa, amma idanuwan masu hikima da kasashen duniya sun bude kan lamarin.

Ya bukaci ‘yan Najeriya su yi addu’a domin tabbatar da cewa mulki ya sauya zuwa hannun da jama’a za su amince da shi.

A cewarsa:

“Zai yi kama da zabe ne, amma ba zai zama zabe na gaskiya ba idan aka yi magudi, amma talakawa za su nuna rashin amincewa.

Kara karanta wannan

"Idonmu na kan ku": Kwankwaso ya tura sako bayan zanga zangar adawa da matakin INEC

“Ku saurara, zaben 2027 ba wai game da Peter Obi kadai ba ne. Duk wani kuskure na magudi, wani abu da bai taba faruwa ba, zai faru a wannan kasa. Wannan shi ne sakon da nake dauke da shi.

Ya kammala da cewa sakon da ya kawo daga Ubangiji shi ne a tabbatar da adalci domin ganin an samu sahihin sauyin mulki a kasar.

Matasa sun goyi bayan takarar Jonathan

A wani labarin, an ji cewa wasu matasa sun cika gidan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Abuja a kan batun zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Masu zanga-zangar sun ce sun yi shawarwari a fadin ƙasa kafin neman Jonathan ya dawo kujerarsa ta shugabancin kasa.

An tabbatar da cewa Jonathan bai gana da matasan ba, amma ana ci gaba da matsa masa lamba ya dawo siyasa a dama da shi a zaɓen 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.