Gawuna da Fitaccen Malami a Kano Sun Ja Tawaga zuwa Gidan Kwankwaso

Gawuna da Fitaccen Malami a Kano Sun Ja Tawaga zuwa Gidan Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya shiga jam'iyyar ADC na cigaba da karbar mutane a gidan shi da ke birnin tarayya Abuja
  • Nasiru Yusuf Gawuna da ya yi wa jam'iyyar APC takarar gwamna a Kano a 2023 ya ziyarci Rabiu Kwankwaso tare da wata tawaga ta musamman
  • Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi magana kan ziyarar da Gawuna ya kai wajen Madugun Kwankwasiyya a Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Siyasar Kano na cigaba da daukar sabon salo, inda aka hango Sanata Rabiu Kwankwaso tare da Nasiru Yusuf Gawuna a Abuja bayan shiga ADC.

Nasiru Gawuna da ya ke cikin manyan APC a jihar Kano a sauya sheka zuwa ADC bayan Abba Kabir Yusuf ya shiga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Idonmu na kan ku": Kwankwaso ya tura sako bayan zanga zangar adawa da matakin INEC

Rabiu Musa Kwankwaso da tawagar Nasiru Yusuf Gawuna
Rabiu Kwankwaso da tawagar Nasiru Gawuna bayan ganawa a Abuja. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai game da ganawar Kwankwaso da Nasiru Gawuna a cikin wani sako da Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa ma X.

Gawuna ya gana da Kwankwaso a Abuja

A ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilun 2026 Nasiru Yusuf Gawuna ya ja wata kwarya-kwaryar tawaga zuwa gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Abuja.

Sanarwar da hadimin Kwankwaso ya fitar ta nuna cewa:

"Mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya karɓi bakuncin Dr. Nasiru Yusuf Gawuna tare da Sheikh Ishaq Adam a gidansa da ke Maitama, Abuja."

Martanin hadimin Abba Kabir Yusuf

Da yake mayar da martani, mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi magana a Facebook yana nuna cewa tawagar ba wata mai karfi ba ce, inda ya ce:

“Yau dai Baba Gawuna ya cire tsoro ya kai wa Madugu gaggan mutanen da ya shiga ADC da su mutum bakwai. Don Allah ku daina cewa da mutum 3 ya shiga, su 7 ne cif.”

Kara karanta wannan

Nafiu Bala: Kwankwaso ya mika bukatar ceto jam'iyyar ADC ga Sarkin Gombe

Kwankwaso ya karbi wasu zuwa ADC

Bayan Nasiru Gawuna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi Hon. Nura Sani Yanchibi a gidansa da ke Maitama a Abuja a daren Alhamis.

Hon. Yanchibi, wanda ya kasance ɗan takarar PDP na mazabar Tsanyawa/Ghari a zaɓen 2023, ya sauya sheka a hukumance zuwa jam’iyyar ADC.

Haka kuma, Kwankwaso, PhD, FNSE, ya karɓi Alhaji Ahmad Balarabe Bello, shugaban kamfanin Amnur Agro Allied, a gidansa.

An tarbi Alhaji Bello da kwanan nan ya sauya sheka zuwa ADC hannu biyu-biyu a wani taro da ka yi a gidan Sanata Rabiu Kwankwaso.

Ahmad Maiturare Gwale da Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso tare da Ahmad Maiturare Gwale a Abuja. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Har ila yau, Sanata Kwankwaso ya karɓi Hon. Ahmad Maiturare Gwale a wata ziyara ta girmamawa a gidansa da ke Abuja a daren Alhamis.

Nentawe ya yi rawa a gaban Abba

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zai ziyarar aiki jihar Kano.

Shugaban jam'iyyar ya gana da manyan APC a wani taro da ya tika rawa a gaban Abba Kabir Yusuf, inda gwamnan ya rika tafa masa.

'Yan Najeriya da dama sun yi magana kan bidiyon da aka fitar, yayin da wasu ke korafi game da halin da kasa ke ciki wasu kuma ke yaba masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng