Wahalar da na Sha a APC ko Shugaban Jam'iyya bai Sha ba In ji Diyar Buba Galadima
- Zainab Buba Galadima, ɗiyar fitaccen ɗan siyasa ta ce ƴan Najeriya sun janye goyon baya ga shugaba Bola Tinubu
- Ta zargi APC da cin amanar jama’a duk da irin ƙoƙarin da aka yi wajen kawo ta mulki da yi wa mutane dadin baki
- Zainab ta yi gargadin cewa dole jama’a su tashi tsaye kafin zaɓen 2027 domin kare mutuncinsu, su kawar da APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Zainab Buba Galadima, ɗiyar fitaccen ɗan siyasa, Injiniya Buba Galadima, ta bayyana cewa al’ummar Najeriya sun daina mara wa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.
Ta ce wannan ya faru ne sakamakon yadda gwamnati mai ci ta gaza cika alkawuran da aka ɗauka kafin Tinubu ya kama kasar.

Source: Facebook
A wata hira da ta yi da FactNews wacce aka wallafa a shafin Facebook, Zainab ta ce duk da irin ƙarfi da iko da jam’iyyar APC ke da shi, amma talakawan Najeriya ba za su sake amincewa da su ba a zaɓe mai zuwa.
Zainab Buba Galadima ta soki APC
A hirar, Zainab ta jaddada cewa mutane da dama sun sadaukar da rayukansu domin ganin APC ta karɓi mulki a 2023, amma daga bisani aka sakawa jama’a da halin ƙunci da wahala.
Zainab ta bayyana irin asarar da ta yi sakamakon shiga fafutukar siyasa a APC, inda ta ce ta yi ɓari sau biyu, ta rasa dukiya tare da fuskantar matsaloli daban-daban, amma duk da haka ba a samu canjin da ake fata ba.
A cewarta:
"Na rasa abubuwa da yawa, na fi arziki a da fiye da yanzu. Me na ke yi a APC idan ba lokacin wahala ya tashi, lokacin zaɓe ba?"

Kara karanta wannan
2027: Matasa sun yi wa gidan tsohon shugaban kasa tsinke, ana so ya nemi kujerar Tinubu
Ta ƙara da cewa sun bayar da gudunmawa sosai, har ma wasu suka rasa rayukansu domin ganin an samu nasarar APC.
A kalamanta:
"Na bada gudunmawa tsakanina da Allah, da rayuwata da komai. Wasu ma sun rasa ransu. Mun yi wa mutane alƙawari, amma bayan mun samu mulki, duk abin da muka soka a baya sai da muka ninka shi sau 20."
Zainab Galadima ta yi gargadi kan APC
Ta kuma zargi gwamnati da yin watsi da shawarwari da ake bayarwa domin inganta rayuwar talakawa, tana mai cewa hakan ne ya ƙara jefa mutane cikin wahala
Da take magana kan zaɓe mai zuwa, Zainab Buba Galadima ta bayyana cewa akwai yiwuwar a samu yunƙurin murde sakamakon zaɓe, amma ta jaddada cewa dole ne ƴan Najeriya su tashi tsaye domin kare haƙƙinsu.

Source: Twitter
Ta ce idan har jama’a na son tsira da mutuncinsu, wajibi ne su nuna ƙwazo da jajircewa wajen tabbatar da an yi zaɓe cikin gaskiya da adalci.
Zainab ta kuma bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar, inda ta ce mutane da dama na rasa rayukansu sakamakon hare-haren ƴan bindiga.
A cewarta, abin takaici ne yadda mutane ke rayuwa cikin fargaba, ba tare da tabbacin tsira tashe tashen hankula, saboda haka akwai bukatar a canja su.
Jam'iyyar APC ta yi rashin jigo
A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar hamayya ta ADC na kara samun karbuwa, musamman daga wajen 'yan APC da ke ganin ba a yi masu dai-dai ba a yankunansu.
A yanzu haka APC ta rasa tsohon Sanata Kabiru Marafa, ya fice daga jam’iyyar mai mulkin Najeriya zuwa ADC a ranar 9 ga watan Afrilu, 2026.
Wasu daga cikin dalilan da ya bayar na sauya sheka sun hada da zargin shugabancin Bola Tinubu da haddasa rikice-rikice a siyasar Najeriya da koma baya a ƙasa.
Asali: Legit.ng

