Magana Ta Fito: Sanata Ya Bayyana Mutanen da Suka Haddasa Rikicin PDP
- Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Abba Moro, ya yi tsokaci kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP
- Sanata Abba Moro ya bayyana cewa ba wasu ba ne daga waje suka kitsa wutar rikicin da ya dade yana addabar PDP
- Ya bayyana mutanen da ke cikin jam'iyyar wadanda ke da alhaki a rikicin da ya dade yana ci ba tare da kawo karshensa ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro, ya yi magana kan rikicin da ya dade yana addabar jam'iyyar PDP.
Sanata Abba Moro ya ɗora alhakin rikicin PDP a kan ’yan siyasa na cikinta, inda ya jaddada cewa wasu hukumomin waje ba su da sa hannu a kan rashin tabbas ɗin da ake ciki.

Source: Facebook
Sanata Abba Moro ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.
Me Sanata ya ce kan rikicin PDP?
Moro ya ce ƙalubalen da ke addabar PDP da sauran jam’iyyu, mambobinsu ne suka janyowa kansu, ciki har da gwamnoni, ’yan majalisa, da sauran shugabannin jam’iyyar.
“Ina so na bayyana karara cewa ina ganin ’yan siyasa ne ke da alhakin abin da ke faruwa da farko."
"Domin idan ka kalli rikicin, rikicin da ke bayyane a cikin jam’iyyun siyasa, ’yan siyasa ne ke rura wutar sa kuma suke ta’azzara shi.”
- Sanata Abba Moro
Domin ƙara bayyana matsayinsa, ya ƙara da cewa, “Gwamnoni, ’yan majalisa, shugabannin jam’iyya… sune ke da alhakin abin da ke faruwa.”
Shin jam'iyyar PDP ta rabe gida biyu?
Dangane da iƙirarin rarrabuwar kai a cikin PDP, Moro ya yi watsi da ra’ayin cewa jam’iyyar ta rabe zuwa ɓangarori daban-daban.
“To, akwai PDP guda ɗaya ne kawai. Babu biyu."
- Sanata Abba Moro
Wasu abubuwa da suka jawo rikici a PDP
Sanatan ya kuma tabo wasu matakai na baya da jam’iyyar ta ɗauka, musamman babban taron kasa na Ibadan wanda ya haifar da muhawara, inda ya ce taron ya ƙara rura wutar rikicin jam’iyyar saboda rashin bin umarnin kotu.

Source: Facebook
“Kotun ɗaukaka ƙara ta ce taron da aka yi a Ibadan an gudanar da shi ne saɓanin umarnin kotu da ke hana gudanar da shi, saboda haka taron ya zama banza, sannan sakamakonsa ma an soke shi."
- Sanata Abba Moro
A cewarsa, rashin jituwa tsakanin manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da Nyesom Wike da Seyi Makinde, ya taimaka wajen haifar da takun-saƙar da ta sanya zaɓar Ibadan a matsayin wurin taron ya zama abin rigima.
'Dan majalisar PDP ya koma ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki, ya yi murabus daga jam’iyyar PDP.
Abdussamad Dasuki ya sanar da komawarsa jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya bayan raba gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.
'Dan majalisar ya ce ya dauki wannan shawara ne bayan tuntuba da abokai, magoya baya da masu ruwa da tsaki a siyasance.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

