Kujerar Mataimakin Abba Kabir na Neman Jawo Rigima, an Roki Tinubu kan Sule Garo
- Wasu masu ruwa da tsaki a Kano sun bayyana damuwa game da shirin kakaba sabon mataimakin gwamna a jihar
- Kungiyar ta rubuta wa Bola Tinubu wasiƙa mai zafi, tana zargin akwai matsin lamba domin tilasta nada mataimakin gwamna
- Ta ce matakin na iya lalata martabar gwamnati da APC, tare da jawo matsalar siyasa yayin da ake shirin zaben 2027
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu masu ruwa da tsaki a Kano sun aika wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu budaddiyar wasika kan siyasar jihar da ke faruwa.
Wasikar na dauke da zarge-zarge kan kokarin tilasta wa Gwamna Abba Kabir Yusuf nada mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo mai fuskantar tuhumar cin hanci.

Source: Facebook
Hakan na cikin wasikar da Habib Musa Dawanan ya sanya wa hannu, wanda Legit.ng ta samu inda suka yi korafin kakaba mataimakin gwamna.
An yi gargadi kan nada Garo mataimakin gwamna
Sun bayyana wannan yunkuri a matsayin “hari kai tsaye ga bin doka,” suna gargadin cewa hakan zai iya dakatar da shari’o’in da ake yi musamman da suka shafi cin hanci.
Sun yi zargin cewa mutumin da ake son nada wa yana cikin wadanda ake tuhuma a wasu manyan shari’o’in cin hanci da gwamnatin Kano ta shigar a kotu.
A cewarsu, wannan mataki zai zama nuna bambanci, musamman bayan tsohon mataimakin gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi murabus sakamakon irin wadannan zarge-zarge.
Kungiyar ta kara da cewa nada wani da ake tuhuma zai rage darajar gwamnatin Kano da jam’iyyar APC, tare da kawo cikas ga kokarin yaki da cin hanci na gwamnatin Tinubu.
Sun kuma gargadi cewa irin wannan matsin lamba na iya jawo matsalar siyasa, ganin cewa ‘yan adawa na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zabukan gaba a jihar.

Source: Twitter
Kujerar mataimakin gwamna: Bukatar yan Kano ga Tinubu
A cikin wasikar, sun ce wannan yunkuri kamar wata dabara ce ta bai wa wanda ake tuhuma kariya ta bayan fage daga hukunci.
Sun yi gargadin cewa hakan zai zubar da mutuncin ofishin gwamna tare da raunana tsarin majalisar dokoki.
Masu ruwa da tsakin sun kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar da daidaito wajen yaki da cin hanci, suna misalta binciken da ake yi wa wasu manyan tsofaffin jami’ai a matakin tarayya.
A karshe, sun bukaci shugaban kasar da ya bar Gwamna Yusuf ya zabi mataimakinsa ba tare da tsoma baki ba, suna jaddada muhimmancin kare mutuncin hukumomi da tsarin mulki.
Matsayar Garo kan zuwan Abba Kabir APC
An ji cewa Murtala Sule Garo ya yi maraba da sauya shekar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin kasa.
Garo, wanda ya yi takarar mataimakin gwamna a zaben 2023 karkashin inuwar APC, ya ce Abba ya dauki matakin da ya dace a siyasance.
Tsohon kwamishinan ya ce matakin da gwamna ya dauka ya nuna irin gogewarsa a fagen siyasa, wanda hakan zai amfanar da jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

