Za a Jika wa APC Aiki, Tsohon Jagoran Yakin Neman Zaben Tinubu a Zamfara Ya Koma ADC

Za a Jika wa APC Aiki, Tsohon Jagoran Yakin Neman Zaben Tinubu a Zamfara Ya Koma ADC

  • Jam'iyyar hamayya ta ADC na kara samun karbuwa, musamman daga wajen 'yan APC da ke ganin ba a yi masu dai-dai ba a yankunansu
  • A yanzu haka APC ta rasa tsohon Sanata Kabiru Marafa, ya fice daga jam’iyyar mai mulkin Najeriya zuwa ADC a ranar 9 ga watan Afrilu, 2026
  • Wasu daga cikin dalilan da ya bayar na sauya sheka sun hada da zargin shugabancin Bola Tinubu da haddasa rikice-rikice a siyasar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Tsohon sanata kuma tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu/Shettima a jihar Zamfara, Kabiru Marafa, ya fice daga APC.

Jigon kuma babban 'dan siyasa a Najeriya ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

Bayan Yusuf Buhari, dan sarkin Daura zai fito takara a 2027

Marafa ya hakura da Tinubu da APC, ya sauya sheka
Sanata Kabiru Marafa ne jihar Zamfara, Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Senator Kabiru Garba Marafa
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa Marafa, wanda ya taba rike mukamin kwamishina a Zamfara, ana masa kallon daya daga cikin manyan magoya bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a yankin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Bola Tinubu ya rasa jigon APC a Zamfara

Yayin da yake sanar da sauya sheƙarsa, Marafa ya zargi shugaban kasa Tinubu da kokarin jefa rudani a tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

Ya ce matakin da ya dauka ya biyo bayan wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jihar Kaduna, inda ya tattauna da abokan siyasa da magoya bayansa.

A cewar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mansur Haruna:

“Bayan tattaunawa mai zurfi da nazari kan makomar tafiyar siyasa, Sanata Marafa ya sanar da kudurinsa na shiga jam’iyyar ADC.”
Marafa ya zargi Tinubu da hada rikici a siyasar Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yana addu'a bayan sallah a masallaci Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Har ila yau, a yayin taron, Marafa ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da yin magudin siyasa, ciki har da yunkurin amfani da bayanan lambar shaidar kasa (NIN) wajen rajistar ‘yan jam’iyya ta hanyar bangaranci.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya fara shiga matsala a Isra'ila ana cigaba da yakar Iran da makwabtan kasashe

Ya kara da cewa, duk wani matsin lamba ko rikicin siyasa ba zai hana shi ci gaba da wannan tafiya ba, yana mai jaddada cewa wannan mataki na nufin kubutar da al’umma daga abin da ya kira “bautar siyasa.”

Rikicin siyasar Marafa a jam'iyyar APC

Sanata Marafa ya taba neman takarar gwamna a karkashin APC a shekarar 2019, amma bai samu goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari ba.

Wannan rashin jituwa ya haifar da rikici mai tsanani a jam’iyyar, inda aka samu bangarori biyu masu adawa da juna.

Daga bisani, Marafa ya kai karar jam’iyyar APC kotu, yana kalubalantar yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani.

Lamarin ya kai har Kotun Koli, wacce ta yanke hukunci cewa ba a gudanar da zaben fitar da gwani yadda ya kamata ba. Sakamakon haka, an bai wa jam’iyyar PDP dukkannin kujerun da APC ta lashe a zaben.

Marafa ya fadi makomar Tinubu

A baya, mun wallafa cewa Sanata Kabiru Garba Marafa na jihar Zamfara ya yi gargadi a kan makomar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da ake shirin gudanar da babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

APC ta karbe ikon majalisa gaba daya da mamban PDP tilo ya koma jam'iyyar

Ya yi gargadin cewa Shugaba Tinubu zai iya fuskantar ƙalubale wajen samun ƙuri’un Arewa a zaɓen 2027 saboda abubuwa da ake ganin ba ya kyauta wa mutanen yankin ba, kuma za su rama.

Sanata Kabiru Garba Marafa ya ce akwai barazanar Shugaban Ƙasa zai rasa goyon bayan yawancin ‘yan Arewa a 2027 idan abubuwan da ake gani yanzu ba su sauya kafin lokacin ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng