Dalilin da Ya Sanya Jagororin PDP Suka Gana da Kwankwaso, Atiku, Obi a Abuja

Dalilin da Ya Sanya Jagororin PDP Suka Gana da Kwankwaso, Atiku, Obi a Abuja

  • Wani ɓangare na jam'iyyar PDP ƙarƙashin Gwamna Seyi Makinde ya ziyarci jagororin ADC domin tattauna matsin lambar da hamayya ke fuskanta
  • Manyan jagororin jam'iyyar adawa ta ADC da suka haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rabiu Kwankwaso ne suka karɓi bakuncin tawagar PDP
  • Sai dai, tsagin PDP na Nyesom Wike ya nesanta kansa da ziyarar, yana mai cewa masu taron sun wakilci kansu ne, ba jam'iyyar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Siyasar Najeriya ta ɗauki sabon salo yayin da wani ɓangare na PDP ya kai ziyarar ban-girma ga jagororin jam'iyyar ADC a wani yunƙuri na nuna goyon baya ga juna.

Wannan ziyara, wadda sakataren yaɗa labarai na ɓangaren PDP, Ini Ememobong, ya tabbatar, ta biyo bayan abin da suka kira "hare-haren siyasa" da ake kai wa jam'iyyun hamayya a ƙasar.

Kara karanta wannan

'Dan marigayi Buhari ya amsa kira, ya bayyana kujerar da zai nema a zaben 2027

Jagororin PDP sun kai ziyarar karfafa gwiwa ga jagororin ADC
Jagororin PDP tare da jagororin ADC a gidan David Mark a Abuja bayan zanga-zangar kare dimokuradiyya. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Jagororin PDP sun gana da su Atiku

Tawagar PDP, ta samu jagorancin Gwamna Seyi Makinde tare da tsohon shugaban majalisar dattawa Adolphus Wabara da tsohon Gwamna Jerry Gana, in ji rahoton Punch.

Jagororin sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ƙoƙarin raunata dimuƙuraɗiyya, ta hanyar kokarin murkushe jam'iyyun adawa.

Sun yi gargaɗi cewa muddin aka ci gaba da matsa wa bangaren hamayya lamba, hakan zai iya shafar tsarin jam'iyyu da dama a Najeriya baki ɗaya.

Sanarwar Ini Ememobong ta ce:

"Shugabannin jam'iyyar PDP sun kai ziyarar ban girma ga shugabannin ADC kan hare-haren siyasa da ake kai wa jam'iyyun hamayya a Najeriya."

Haɗuwar manyan jagororin hamayya

Wani abin lura a wannan taro shi ne yadda manyan jagororin siyasar Najeriya waɗanda suka fice daga jam'iyyar PDP, NNPP, LP ne dai suka karɓi bakuncin tawagar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jagororin ADC da suka halarci taron sun haɗa da Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Ƙasa da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban kasa na LP a 2023.

Kara karanta wannan

"Allah na fushi da Kwankwaso," NNPP ta fadi dalilin rikicin da ya taso a ADC

Sauran sun hada da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa karkashin NNPP a 2023 da kuma David Mark, shugaban ADC da tsohon minista, Rotimi Amaechi.

A martaninsu, jagororin ADC sun nuna jin daɗinsu kan wannan ziyara, inda suka nanata cewa akwai barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya muddin ba a kare haƙƙin jam'iyyun hamayya ba.

Jagororin PDP da ADC sun yarda cewa jam'iyyun adawa na fuskantar hare haren siyasa.
Hagu zuwa dama: Atiku Abubakar, Gwamna Seyi Makinde da David Mark a taron jagororin APC da ADC. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Martanin bangaren Nyesom Wike

To sai dai kuma, PDP, bangaren Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, ya fito ta nesanta kanta daga wannan tattaunawa.

Sakataren yaɗa labarai na wannan tsagi, Jungudo Mohammed, ya fitar da sanarwa a yau inda ya ce PDP ba ta da masaniya, kuma ba ta ba da izinin wata ganawa da jam'iyyar ADC ba.

Ya bayyana cewa duk wanda ya halarci wannan taro ya yi hakan ne a matsayin kansa, kuma hakan ba ya wakiltar matsayar jam'iyyar PDP baki ɗaya.

Sakon Kwankwaso bayan zanga-zangar ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da bangarenci gabanin 2027.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Jam'iyyar adawa ta roki Kwankwaso, Atiku da Obi su dawo cikinta

Ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya hadu da Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu manyan ADC sun yi zanga-zanga a Abuja.

Bayan tattakin lumana da suka yi a babban birnin tarayya Abuja, Sanata Kwankwaso ya aika wa INEC sakon kar-ka-kwana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com