'Idonmu na Kan ku': Kwankwaso Ya Tura Sako bayan Zanga Zangar Adawa da Matakin INEC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da bangarenci gabanin 2027
- Ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya hadu da Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu manyan ADC sun yi zanga-zanga a Abuja
- Bayan tattakin lumana da suka yi a babban birnin tarayya Abuja, Sanata Kwankwaso ya aika wa INEC sakon kar-ka-kwana
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya nuna bangaranci karara da hukuma zabe ta INEC ke yi.
Kwankwaso ya bayyana haka a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu, 2026 bayan shi da wasu manyan ADC sun yi tattakin adawa da yadda INEC ke gudanar da al'amura.

Kara karanta wannan
Netanyahu ya fara shiga matsala a Isra'ila ana cigaba da yakar Iran da makwabtan kasashe

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X na Kwankwaso ya ce ya hada kai da sauran shugabannin hadakar siyasa da kuma masu kishin dimokuradiyya domin yin Allah-wadai da yadda hukumar zabe ta sako ADC a gaba.
Rabiu Kwankwaso ya ja kunnen INEC
A cewarsa, wannan zargi na nuna bangaranci daga INEC na da matukar hadari ga makomar dimokuradiyya a Najeriya.
Ya ce a irin wannan lokaci, dole ne a damu da zargin saboda muhimmancin da hukumar ke da shi wajen tabbatar da sahihin zabe.
Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa, dole ne hukumar ta kasance mai gaskiya da adalci, ba tare da nuna son rai ga kowace jam’iyya ko bangare ba.
Ya bayyana cewa ta haka ne kawai za a tabbatar da cewa an mutunta ra’ayin al’umma idan sun kada kuria'arsu.
'Dalilin tattakinmu' - Sanata Kwankwaso
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa tattakin lumana da aka gudanar a Abuja ya hada kungiyoyi daban-daban na ‘yan adawa, inda suka aika sako karara ga hukumomi.

Source: Facebook
Ya ce tattakin ya nuna cewa ba za su zuba ido kawai ba yayin da ake zargin hukumar zabe da tauye muradin jama’a.
A cewarsa, hadin kan da aka nuna a wannan tattaki alama ce ta cewa ‘yan Najeriya na da niyyar kare dimokuradiyyarsu.
Kwankwaso ya kara da cewa za su ci gaba da bibiyar dukkannin ayyukan INEC domin tabbatar da cewa ta koma kan turbar da ta dace.
Ya bukaci hukumar da ta dauki matakin gaggawa domin gyara duk wani gibi da ake zargin akwai, yana mai cewa hakan ne kadai zai tabbatar da ci gaban dimokuradiyya a Najeriya.
Kwankwaso su na nan a ADC
A baya mun wallafa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi hira ta musamman game da rikicin da ya bulla jam'iyyar ADC bayan sauya sheka daga NPPP.
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan takarar zaben 2027, inda aka masa tambayoyi kan yiwuwar zama mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan siyasa da dama ke shirye-shirye domin samun nasara a zaben 2027 a matakai daban-daban a kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
