APC: Nafi'u Bala Ya Yi Bayani game da Zargin Karɓo Kwangilar Lalata ADC

APC: Nafi'u Bala Ya Yi Bayani game da Zargin Karɓo Kwangilar Lalata ADC

  • Shugaban tsagin ADC na kasa Nafi’u Bala, ya zargi sababbin shigowa jam'iyyarsu da haddasa rikice-rikice
  • Ya ce tsofaffin ‘yan jam’iyya sun dade suna tafiyar da ADC cikin lumana kafin zuwan mutanen da aka ba su mafaka
  • Nafi'u Bala ya yi magana game da zargin cewa ya karbo wata kwangila ne domin ya hana 'yan adawa katabus gabanin zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe – Shugaban tsagin jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala, ya zargi mutanen da suka shigo cikin jam’iyyar da haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyunsu na asali.

Ya bayyana haka ne duk da ya ki sauraren kiran da ake yi masa na a zauna a tattauna matsalolin da suka sa shi adawa da shugabancin David Mark.

Kara karanta wannan

Nafi'ua Bala: "Abin da ya hana ni amsa gayyatar Kwankwaso"

Nafiu Bala ya yi kaca-kaca da yan adawa
Alamar jam'iyyar APC a hagu, Nafiu Bala a dama Hoto: ADC Party
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Nafi’u Bala ya yi zargin cewa wadannan mutane na kokarin dunkule kansu ne a cikin jam’iyyar da ya ce sun dade suna jagoranci a cikinta.

Nafi'u Bala ya soki sababbin 'yan ADC

A tattaunawarsa da Legit, Nafi’u Bala ya bayyana cewa wasu tsiraru daga cikin ‘yan siyasa sun shiga ADC ne bayan sun haddasa rigingimu a jam'iyyunsu.

Ya ce wadannan mutane na kokarin hana zaman lafiya da cigaban jam’iyyar, duk da irin kokarin da suka yi na karɓar su domin hadin kai.

Ya bayyana cewa:

"Mu ne halattattun ‘yan ADC shekara da shekaru, kuma muna tafiyar da jam’iyyar nan lafiya cikin lumana, amma wadanda ba ‘yan jam’iyyarmu ba, wadanda rana tsaka suka hada rigingimu a jam’iyyunsu, suka yanke hukunci za su shigo jam’iyyarmu, muka ba su dama mu hadu domin Najeriya ta kasance kasa daya, kwatsam sai suka ayyana kansu a matsayin shugabanni."

Kara karanta wannan

Netanyahu ya fara shiga matsala a Isra'ila ana cigaba da yakar Iran da makwabtan kasashe

Martanin Nafiu game da karbo kwangila

A wani bangare, Nafi’u Bala ya musanta zargin cewa yana aiki da jam’iyyar APC mai mulki domin kawo cikas ga cigaban ADC mai adawa a Najeriya.

Ya bayyana cewa wannan zargi ba shi da tushe balle makama, yana mai cewa babu wata alaƙa da ke tsakaninsa da APC kamar yadda ake yadawa.

Nafiu Bala ya karyata alaka da APC
Shugaban APC na kasa, Yilwatda Nentawe Hoto: Prof Yilwatda Nentawe
Source: Twitter

A cewarsa, ya dade yana fafutukar gina ADC ba tare da wata alaka da wata jam’iyya ba, don haka bai ga dalilin da zai sa ya yi aiki da wata jam’iyya ba domin rusa tasa ba.

Ya ce:

"Duk wanda ya taba gani na da wani dan APC sai ya zo ya fada. Shekara da shekaru muna rike da jam’iyyar nan, ba mu dauke ta muka kai wa APC ba sai a wannan mataki?"

Nafi’u Bala ya kara da cewa masu yada wannan zargi sun rasa abin fada ne, shi ya sa suke kokarin bata masa suna da kirkirar maganganu marasa tushe.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku da Kwankwaso na cikin matsala, ADC ta sake darewa gida 2

Nafiu Bala ya yi biris da Kwankwaso

A baya, kun ji cewa guda daga cikin jiga-jigan ADC Nafi’u Bala ya bayyana cewa ba haka kawai ya yi fatali da kiran da Sanata Rabiu Musa Kwankwas ya yi masa ba.

Ya bayyana haka ne a dai-dai lokacin da jagoran Kwankwasiyya ya bayyana takaicin yadda Nafi'u Bala yaki amsa gayyatar da aka yi masa domin a daidaita.

Nafi'u Bala ya zargi Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran wadanda ke shugabancin ADC a yanzu da kaskantar da su, tare da nuna cewa 'ya'yan talakawa ba su da muhimmanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng